Saurayi ya kashe mahaifin budurwarsa ta hanyar daɓa masa wuƙa yayin da ya kama su suna 'soyewa' a gidansa

Saurayi ya kashe mahaifin budurwarsa ta hanyar daɓa masa wuƙa yayin da ya kama su suna 'soyewa' a gidansa

  • Wani matashi ya yi sanadin rasuwar mahaifin budurwarsa ta hanyar daba masa wuka yayin da suka kacame da dambe
  • Mahaifin budurwar ya yi tafiya ne amma da ya dawo gida sai ya tarar da saurayin tare da 'yarsa suna tsakar more soyayya
  • Hakan yasa suka fara cacan baki daga bisani suka fara dambe shi kuma saurayin ya shiga dakin girki ya dako wuka ya daba wa mahaifin budurwar

Ughelli, Delta - An shiga ruɗani a Otu-Jeremi, hedkwatar ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu, Jihar Delta, a daren ranar Laraba, yayin da wani mutum ya daɓa wa mahaifin budurwarsa wuƙa, rahoton Vanguard.

An gano cewa rikicin ya samo asali ne bayan marigayin, wanda a lokacin haɗa wannan rahoton ba a ga sunansa ba ya dawo daga tafiya ya tarar da wanda ake zargin, Paul, yana soyewa da yarsa.

Kara karanta wannan

Bayan sanar da Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zai gogayya da Tinubu a 2023

Saurayi ya kashe mahaifin budurwarsa ta hanyar daɓa masa wuƙa yayin da ya kama su suna 'soyewa' a gidansa
Mahaifi ya gamu da ajalinsa bayan saurayin 'yarsa ya daba masa wuka. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A yayin da ya ke tambayar abin da ke faruwa, sai suka fara cacar baki daga nan sai dambe ya kaure tsakaninsu.
"A yayin da suke dambe, wanda ake zargin ya daɓa wa mutumin fasashen kwalba. Mutumin ya mutu kafin a kai shi asibiti," in ji majiyar.

'Yan sanda sun tabbatar da kama wanda ake zargi

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Delta, Mr Bright Edafe, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, Vangaurd ta ruwaito.

Amma ya ce:

"Wanda ake zargin ya yi ikirarin ya tafi gidan wata mata. Ya yi ikirarin cewa ya ji kukan yaro, don haka ya shiga gidan ya ɗauki Yaron nan ne mamacin ya shigo ya tambaya 'me ka ke yi da wannan yaron?'
"A hakan ne, suka fara faɗa, wanda ake zargin ya ɗauki wuƙa a ɗakin girki sannan ya ɗaɓa wa mamacin."

Kara karanta wannan

Namijin Kishi: Miji ya dabawa makocinsa wuka har lahira saboda yana sha'awar matarsa

Nasarawa: Yadda mata ta daba wa miji wuka har lahira saboda amsa wayar budurwa

A wani labarin daban, hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Nasarawa ta kama wata mata mai juna biyu mai shekaru 22, Veronica Boniface, saboda kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka saboda ya amsa wayar budurwarsa.

Da ake holen wacce ake zargin a hedkwatan hukumar a Lafia, Kwamandan NSCDC a jihar, Habu Fari, ya ce an kama matar ne a garin Obene a karamar hukumar Keana bayan samun bayanan sirri.

Fari ya yi bayyanin cewa gwaje gwajen da likitoci suka yi wa wanda ake zargin ya nuna cewa ba ta da tabin hankali kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel