Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar

Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya amince da bude gidajen mai da kuma kasuwannin shanu cikin gaggawa
  • A baya gwamnan ya rufe su ne don kawo garanbawul akan matsalar tsaro kamar satar shanu da ta’addanci a fadin jihar
  • Gwamnan ya bayar da umarnin bayan masarautu da dagacin kauyukun da lamarin ya shafa sun tabbatar masa da cewa za su sa ido kwarai

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya amince da gaggawar bude gidajen mai da kasuwannin shanu da a baya aka rufe saboda satar shanu da ta’addanci a jihar, Channels TV ta ruwaito.

Sai dai gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan masarautu biyu da ke jihar sun tabbatar da yadda dagacin kauyukun suka tabbatar da sa ido kuma za su tabbatar ba za a bar wasu harkokin Sarakunan Fawa da sauransu ba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar
Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa ya sa hannu, ya ja kunne inda yace gwamnati za ta kara garkame su matsawar aka lura da wani ta’addanci a jihar.

Tun watan Satumban shekarar da ta gabata aka rufe gidajen mai da kasuwannin shanu don kawo gyara akan matsalolin tsaro a jihar bisa umarnin gwamnati na hana masu kai wa ‘yan bindiga mai da kuma kasuwancin shanun sata a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dokar tsaron ta hada da rufe manyan titina biyu, na Jibia zuwa Gurbin Baure da Kankara zuwa Sheme.

A sabuwar dokar da gwamnatin ta saki, an shawarci baburan haya da su dinga bin titin Funtua amma baburan gida kuma za su iya bin titin Kankara zuwa Sheme.

Bisa yadda dokar tazo, gwamnan ya hana tsayar da ababen hawa a kan kwana ba bisa ka’ida ba da kuma tasoshi har da kasuwannin shanu na kananun hukumomi 14 wadanda suka hada da: Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Malumfashi, Charanci, Mai adua, Kafur, Faskari, Sabuwa, Baure, Dutsinma da Kaita.

Kara karanta wannan

Yajin aikin 'yan adaidaita: PDPn Kano ta zargi Ganduje da shirin karya tattalin arzikin jihar

Ya kara hana yawo da motar shanu da kuma ta itace daga dazuka, sannan an hana mutane 2 zuwa 3 su hau babur a lokaci guda.

Sannan gwamnatin ta hana fiye da mutane 3 hawa keke Napep a lokaci daya da kuma sayar da man fetur a jarkoki.

An dage dokar hana saye da siyarwa a kasuwar tsofaffin babura a Charanchi, Channels TV ta ruwait.

Don datse hanyar kai wa ‘yan bindiga babura da gudun kai wa jama’a farmaki, gwamnan ya ba gidajen mai 2 damar sayar da man fetur kuma kada ya wuce na N5,000 ga ko wanne mutum daya.

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

A wani labari na daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da takwaransa na jihar Zamfara, Bello Matawalle, sun koka akan yadda 'yan ta'adda suke cin karensu babu babbaka a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

Yayin da Zulum yace mayakan ISWAP za su fi tada hankula fiye da Boko Haram ba a Borno kawai ba, har da sauran bangarorin kasar nan idan ba'a kawo karshensu ba, Matawalle ya ce 'yan bindiga da dama ana sakinsu ba tare da mika su gaban kotunan shari'a don a yanke musu hukuncin da ya dace ba, hakan yasa sama da mutane 600,000 suka zama 'yan gudun hijira.

Gwamnan jihar Borno yayi jawabi yayin tarbar kwamitin majalisar dattawa akan al'amuran sojoji a Maiduguri, yayin da Matawalle ya karba tawagar gwamnatin tarayya da ta kai masa ziyarar jaje a Zamfara kan rasin da aka yi na Anka da Bukkuyum a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel