Neja: Ƴan bindiga sun ɗaure ni, ina kallo suka kashe ƴaƴa na 6 ɗaya bayan ɗaya, Dattijo mai shekaru 75

Neja: Ƴan bindiga sun ɗaure ni, ina kallo suka kashe ƴaƴa na 6 ɗaya bayan ɗaya, Dattijo mai shekaru 75

  • Farmakin da ‘yan bindiga suka kai Kauyen Nakuna da Wurukuchi da ke karamar hukumar Shiroro a ranar Talata ya girgiza jama’a da dama
  • Sakamakon farmakin, sun halaka mutane da dama ciki har da yaran wani Mallam Yahaya Mota Nakuna mai shekaru 75 kamar yadda ya shaida wa manema labarai
  • Ya ce sun je gona ne don yin girbi ashe wahala tana gaba, anan ‘yan bindigan suka ritsa su suka daddaure shi sannan su ka halaka yaransa 6 a gaban idonsa

Jihar Neja - A ranar Talata ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Nakuna da Wurukuchi da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar wacce suka janyo asarar rayuka da dama, The Nation ta ruwaito.

Babban tashin hankalin ya ritsa da wani Mallam Yahaya Mota Nakuna mai shekaru 75 wanda a gaban idonsa suka halaka yaransa daya bayan daya.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan ta'adda suka bindige mutane 13 har lahira a harin Jihar Neja

Neja: Ƴan bindiga sun ɗaure ni, ina kallo suka kashe ƴaƴa na 6 ɗaya bayan ɗaya, Dattijo mai shekaru 75
Neja: Ƴan bindiga sun ɗaure ni, ina kallo suka halaka yra na 6 ɗaya bayan ɗaya, Dattijo mai shekaru 75. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Yayin da Yahaya ya ke tattaunawa da wakilin The Nation, ya ce sun bar gida zuwa gona a ranar Talata ba tare da sanin babban tashin hankalin da zai same su ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, suna tsaka da girbin shukokinsu ‘yan bindiga suka isa har gonar tasu suka tambayesu inda ‘Yan Sa Kai suke, shi ne suka shaida musu cewa ba su gansu ba.

Ya ce da sun san abinda zai faru da tserewa suka yi bayan ganinsu

Kamar yadda ya ce:

“Bamu san abinda ya kawo su ba lokacin da suka zo suna tambayar inda ‘Yan Sa Kai suke, kuma mun fada musu gaskiyar abinda muka sani.
“Da mun san abinda ya kawo su gonarmu da mun tsere daga isowarsu. Don tsawon shekaru dama guduwa muke yi idan mun gansu.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Akalla mutum 17 sun mutu, yayin da yan bindiga suka cinnawa gidaje wuta a Filato

Yahaya ya shaida yadda yaransa 6 suke tare da shi don taya shi girbin, inda yace ko guda daya bai tsira ba a cikinsu.

Ya ce take anan ‘yan bindiga suka daure masa hannayensa kuma a gaban idonsa suka halaka yaran nasa daya bayan daya.

Cike da hawaye tsohon yake shaida cewa:

“Bayan mun sanar musu da cewa bamu san inda ‘Yan Sa Kai suke ba sai suka tura yarana cikin kauyen da hannayensu daure sannan suka fille musu kai tare da harbin wasu mutane 9 a kawunansu. Bayan nan ne suka kwance min hannaye na suka ce in tafi.”

Ya ce sun kwashe sa’o’i 5 suna haka kaburburan yaransa shi da dan uwansa

Ya ce bayan sun tafi ya gayyaci dan uwansa daga kauyen da ke makwabtaka da su don taya shi birne yaran nasa.

Ya bayyana yadda suka kwashe sa’o’i 5 su biyu suna haka kaburburan yaran nashi cike da kunci da takaici da rashin sanin ta inda zai fara.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida, Salisu Maki, a Nasarawa

Yanzu haka Yahaya yana zama a garin Zumba tare da sauran wadanda harin ranar Talata ya ritsa da su.

Da misalin karfe 11 na safe ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Nakuna da Wurukuchi a ranar Talata kuma yawanci manoma harin ya fi shafa.

Mazaunan kauyakun sun ce mutane 37 ne suka rasa rayukansu, amma kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas ya ce mutane 13 ne kacal suka rasa rayukansu.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel