Mutane 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon mummunan hatsarin mota a Adamawa

Mutane 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon mummunan hatsarin mota a Adamawa

  • Mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani kazamin hatsarin da ya auku a babban titin Yola zuwa Mubi cikin jihar Adamawa
  • Lamarin ya auku ne bayan motoci biyu sun ci karo da juna da misalin karfe 3 na ranar Alhamis a dai-dai kauyen Golontabal da ke karamar hukumar Song
  • Wata bas ce ta taho da gudu yayin da wata Toyota ma ta taho su ka ci karo suna fuskantar juna, kuma duk motocin cike suke makil da fasinjoji

Jihar Adamawa - Mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin da ya auku a babban titin Yola zuwa Mubi da ke jihar, The Nation ta ruwaito.

Motoci biyu wadanda suka taho ta bangarori daban-daban suka ci karo nan da nan su ka kama ci da wuta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Mutane 12 sun kone kurmus sakamakon mummunan hatsarin mota a Adamawa
Rayyuka 12 sun salwanta sakamakon mummunan hatsarin mota a Adamawa. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Wakilin The Nation ya gano yadda lamarin ya auku da misalin karfe 3 na ranar Alhamis wuraren kauyen Golontabal da ke karamar hukumar Song.

Motocin haya ne cike makil da mutane

Hatsarin ya auku da mota hummer bus mai lambar rijista GME 944 XC da wata Toyota Corolla mai lamba YLA 388HS.

Duk motocin haya ne wadanda suke cike makil da fasinjoji.

An samu bayanai a kan yadda motar bas din ta nufi Yola, babban birnin jihar Adamawa daga karamar hukumar Uba da ke jihar Borno.

Dayar Toyotar kuma ta nufi Mubi, arewacin Jihar Adamawa daga Jabbi Lamba a karamar hukumar Girei kusa da Yola.

Mutane 12 ne suka kone kurmus

Kamar yadda wani ganau ya shaida:

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

“Motocin sun ci karo ne yayin da suke fuskantar juna daga nan suka kama da wuta inda fasinjoji 8 har da direba suka rasa rayukansu.”

A cewar ganau din, fasinjoji 3 da direban sun mutu cikin Toyota Corollar, wanda gabadaya idan aka kirga sun cika mutane 12.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar hatsarin.

A cewarsa Nguroje, an tafi da gawawwakin zuwa asibitin Song Cottage sannan ana ci gaba da binciken asalin tushen hatsarin.

Nguroje ya yi wa ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu ta’aziyya sannan ya ja kunne akan tukin ganganci.

Mutane 16 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi, Hukumar FRSC

A wani labarin, babban kwamandan Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce a kalla mutane 16 ne suka rasu a hatsarin mota da ya faru a jihar a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Akalla mutum 17 sun mutu, yayin da yan bindiga suka cinnawa gidaje wuta a Filato

Mr Abdullahi ya tabbatar da hakan ne cikin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, a ranar Litinin a Bauchi, Premium Times ta ruwaito.

A cewarsa, hatsarin, wanda ya ritsa da babban mota da motar haya ta Toyota Hummer bus, ya faru ne a kauyen Bambal a hanyar Kano zuwa Jama'are misalin karfe 7 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel