Mutane 16 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi, Hukumar FRSC

Mutane 16 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi, Hukumar FRSC

  • Mutane a kalla 16 ne suka riga mu gaskiya sakamakon hatsarin mota a ranar Lahadi a jihar Bauchi
  • Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, a Jihar Bauchi ta bakin kwamandanta, Yusuf Abdullahi ta tabbatar da lamarin
  • Abdullahi ya ce gudu fiye da ka'ida ne ya janyo hatsarin ya kuma yi kira ga direbobi su rika bin dokokin tuki a yayin da suke tafiye-tafiye

Bauchi - Babban kwamandan Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce a kalla mutane 16 ne suka rasu a hatsarin mota da ya faru a jihar a ranar Lahadi.

Mr Abdullahi ya tabbatar da hakan ne cikin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, a ranar Litinin a Bauchi, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Mutane 16 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi, Hukumar FRSC
Hatsarin mota ya kashe mutum 16 a Jihar Bauchi, FRSC. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

A cewarsa, hatsarin, wanda ya ritsa da babban mota da motar haya ta Toyota Hummer bus, ya faru ne a kauyen Bambal a hanyar Kano zuwa Jama'are misalin karfe 7 na dare.

Kwamandan, wanda ya ce jami'ansa sun shafe minti bakwai kafin su isa wurin ya ce gudu fiye da kima da direbobin ke yi ne ya janyo hatsarin, rahoton Premium Times.

Ya ce:

"Mutane 16 ne hatsarin ya ritsa da su, 10 daga cikinsu maza sai kuma mata shida sannan dukkansu sun rasu.
"Hummer bus din ta kama da wuta bayan ta yi karo da babban motar kuma babu ko mutum daya da ya rayu bayan hatsarin.
"Wasu daga cikin mutanen da ke cikin Hummer bus din sun kone kurmus ba a iya gane su."

Kara karanta wannan

An Bindige Jami'in FRSC Har Lahira A Kofar Gidan Abokinsa

Ya bayyana cewa an kai gawarwakin dakin ajiye gawa na babban asibitin Kiyawa da ke hanyar Kano zuwa Jama'are.

Kwamandan ya shawarci masu ababen hawa su rika takatsantsan sannan su dinga bin dokokin tuki a hanya.

Hatsarin mota ya lakume rayuka 6 tare da jikkata 19 a jihar Bauchi

A wani labarin, rahotanni sun kawo cewa rayuka shida sun salwanta sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Bauchi a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba.

Lamarin ya rutsa ne da wasu motocin haya guda biyu. Kwamandan hukumar kula da hana afkuwar hatsarurrukan hanya reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Litinin, jaridar Punch ta rahoto.

A cewarsa, wasu mutane 19 sun jikkata a lamarin wanda ya afku a kauyen Durum da ke hanyar Bauchi zuwa Kano.

Lamarin na zuwa ne kasa da kwanaki hudu bayan wasu mutane biyar sun mutu sannan uku suka jikkata a wani mummunan hatsari da ya wakana a kauyen Gubi, hanyar babban titin Bauchi-Kano.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ba Zan Ajiye Aiki Ba Kan Yawaitar Tserewar Fursunoni Daga Gidan Yari, Ministan Buhari

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel