Babbar magana: Wani jirgin saman Arik daga Legas ya yi hadari, ya sauka a Asaba

Babbar magana: Wani jirgin saman Arik daga Legas ya yi hadari, ya sauka a Asaba

  • Wani jirgin saman kamfanin Arik da ya taso daga jihar Legas ya yi hatsari a wani yankin Asaba na jihar Delta
  • Rahoto ya shaida cewa, wata jarumar fina-finan Nollywood da ke cikin jirgin ta bayyana faruwar lamarin
  • Ya zuwa yanzu, hukumomin jirgin saman Arik da tashar jirgin saman basu fitar da sanarwa kan lamarin ba

Asaba, Delta - Daya daga cikin kamfanonin jiragen saman Najeriya, Arik Air da ya tashi daga Legas zuwa Asaba kana ya yi hatsari a wani yanki mai nisa a babban birnin jihar Delta da ke Kudu maso Kudu.

Rahotanni sun nuna cewa sama da fasinjoji 25 ne suka shiga jirgin da misalin karfe 6 na yamma a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya.

Jirgi ya fadi a jihar Delta
Babbar magana: Wani jirgin saman Arik daga Legas ya yi hadari, ya fadi a Asaba | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

AIT ta ce ta yi kokarin tabbatar da labarin daga mahukuntan kamfanin amma hakan bai samu ba. Sai dai daya daga cikin jaruman fina-finan Nollywood, Uche Elendu, wacce tana daya daga cikin fasinjojin ta ce sun tsallake rijiya da baya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

Elendu wacce nan take bayan faruwar lamarin ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta caccaki ma’aikatan jirgin, inda ta ce saura mintuna 10 su isa filin jirgin saman Asaba lokacin da aka samu matsalar.

Ta kara ba da labarin abin da ta gani na ban tsoro cewa matukin jirgin ya yi yunkurin komawa jihar Legas kafin hatsarin ya faru duk da cewa sun kusa isa filin jirgin saman na Asaba.

Ta ce daya daga cikin ma’aikatan jirgin ya gaya mata tun a farko cewa ta ajiye kayanta a karkashin kujera cewa zai cece ta idan da jirgin zaiyi hatsari amma ta hana shi ci gaba da batu irin wannan.

Sabanin ikirarin Elendu, kamfanin jirgin a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsu na Instagram ranar Laraba, ya bayyana cewa jirgin ya sauka lafiya a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

Jaridar Punch ta rahoto daga sanarwar cewa:

“Daya daga cikin jirgin mu dash 8 Q-400 da ke aiki tsakanin Legas zuwa Asaba a yammacin yau ya dawo sansaninsa saboda wata matsala da aka samu.
“Jirgin ya sauka lafiya, kuma matukin jirgin, bisa bin ka’idojin tsaro, ya yanke shawarar sauke fasinjojin a bakin filin jirgi na Murtala Muhammed. Daga baya an kai jirgin na Arik Air wajen ajiya don aikin kula da shi.”

Da yake ba da hakuri kan abin da ya faru, kamfanin ya ce ya samar da wani jirgin da zai maye gurbinsa ga fasinjojin da abin ya shafa.

Janar Attahiru ya zama shugaban soji na biyu da ya mutu a hadarin jirgi

A wani labarin, juma'ar yau bata yiwa yan Najeriya dadi ba yayinda shugaban hafsoshin Sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya mutu tare da wasu manyan hafsoshi a hadarin jirgin saman.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda ginin wurin Ibada ya hallaka mutane suna tsaka da bautar Allah

Duk da cewa ba'a samu cikakken bayanin abinda ya faru har yanzu ba, hukumar Sojin saman Najeriya ta tabbatar da faruwar wannan hadari.

Janar Attahiru ne mutum na biyu da ya mutu kan wannan kujera sakamakon hadarin jirgi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel