Janar Attahiru ya zama shugaban soji na biyu da ya mutu a hadarin jirgi

Janar Attahiru ya zama shugaban soji na biyu da ya mutu a hadarin jirgi

- Shugaban hafsoshin sojin kasan Najeriya, Laftanan Ibrahim Attahiru ya rigamu gidan gaskiya

- Attahiru ya mutu tare da iyalinsa cikin jirgin saman a ranar Juma'a a Kaduna

- Attahiru ne shugaban Soji na biyu da ya mutu sakamakon hadarin jirgi a tarihin Najeriya

Juma'ar yau bata yiwa yan Najeriya dadi ba yayinda shugaban hafsoshin Sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya mutu tare da wasu manyan hafsoshi a hadarin jirgin saman.

Duk da cewa ba'a samu cikakken bayanin abinda ya faru har yanzu ba, hukumar Sojin saman Najeriya ta tabbatar da faruwar wannan hadari .

Janar Attahiru ne mutum na biyu da ya mutu kan wannan kujera sakamakon hadarin jirgi.

Na farko shine Laftanan Kanar Joseph Akahan wanda shine shugaban hafsoshin Soji tsaknain Mayun 1967 da Mayun 1968 lokacin da ya mutu a hadarin jirgi mai saukar angulu lokacin yakin basasa.

Akahan wanda dan asalin garin Gboko a jihar Benue ne na cikin wadanda suka yiwa Janar Aguyi Ironsi juyin mulki suka dankawa Yakubu Gowon mulki.

An nada shi shugaban hafsoshin Soji ne ana gab da fara yakin basasa.

Lokacin da ya mutu a hadarin jirgin, an maye gurbinsa da Janar Hassan Katsina.

KU KARANTA: Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya ya mutu bayan watanni 4 a ofis

Janar Attahiru ya zama shugaban soji na biyu da ya mutu a hadarin jirgi
Janar Attahiru ya zama shugaban soji na biyu da ya mutu a hadarin jirgi
Asali: Facebook

DUBA NAN: Bamu ce yan Najeriya su mika mana lambobin IMEI dinsu ba, da kanmu zamu dauka, inji NCC

Karo uku kenan a wannan shekarar da jirgin sojin Najeriya zai samu hadari kuma ayi rashin rayukan hafsoshi.

A ranar Lahadi, 21 ga watan Febrairu, jami'an hukumar mayakan sama bakwai sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin Beechcraft KingAir B350i da ya fado a Abuja.

Hakazalika, a ranar Laraba, 31 ga Maris, 2021, jirgin yakin sojin Najeriya Alpha-Jet wanda ke artabu da yan ta'addan Boko Haram ya samu matsala a sararin samaniya kuma yayi hadari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng