Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

  • Shugaban karamar hukuma a jihar Neja ya bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka hallaka mutane
  • Bayan mummunan harin ne gwamnatin jihar ta kafa kwamiti domin binciken musabbin harin tun daga tushe
  • A jawabansa, shugaban karamar hukumar ya bayyana yadda harin ya faru a gaban kwamitin na gwamnatin jihar

Jihar Neja - Shugaban karamar hukumar Mashaegu a jihar Neja, Alhaji Alhassan Isah, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 19 tare da yin garkuwa da 15 a Mazakuka, Kulho, Adogon Malam da kewaye.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana hakan ne jiya Talata 11 ga watan Janairu a lokacin da ya gurfana gaban kwamitin bincike na shari’a da gwamnatin jihar ta kafa kan kashe-kashen.

Ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutane 19 a cikin masallaci yayin harin da suka kai ranar 25 ga Oktoba, 2021, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda ginin wurin Ibada ya hallaka mutane suna tsaka da bautar Allah

Barnar 'yan bindiga a jihar Neja
Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya bayyana 'yan bindiga suka kashe masallata a masallaci | Hoto: channelsyv.com
Asali: UGC

Isah ya ce an kuma kashe mutane biyu da ke kusa da masallacin, yayin da aka yi garkuwa da wasu 15 a nan take.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya ce daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya mutu ne saboda kaduwa sannan ‘yan bindigar suka kashe wasu takwas a daji.

Ya kuma shaida wa hukumar cewa an saki mutane 11 da aka sace bayan biyan kudin fansa da iyalansu suka yi.

Da lauyan da ke wakiltar al'ummar, Barista Bala Ibrahim Zuru ya tambayi shugaban kan ko ya ziyarci sansanin Fulani domin jajanta musu lamarin, Isah ya amsa da cewa tabbas ya je.

Sai dai shugaban ya ce bai ga kowa ba saboda sansanin Fulani ya samu babu kowa a lokacin.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin

Shaidu uku, Idris Umar, wani manomi, Halidu Yusufu da Muhammad Usman da suka bayyana a gaban kwamitin binciken sun tabbatar da kisan da kuma yin garkuwa da mutane da dama a wasu kauyuka a karamar hukumar Masehegu a yayin harin.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Gwamnatin jihar ta kafa kwamitin binciken ne domin tabbatar da ko ‘yan bindiga ne suka aikata kisan ko kuma Fulani ne da ake zargi da kai harin ramuwar gayya a cikin al’umomin da aka samu sabani da su tare da bayyana yankin a matsayin mazauni.

Bayan wannan harin, a watan Disamba an samu aukuwar wani harin 'yan bindiga a masallaci, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da dama, kamar yadda Premium Times ta tattaro.

A wani labarin, Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Maza-Kuka da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja, inda suka kashe wasu masallata 18.

An tattaro cewa, ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne da yawan gaske inda suka far wa mutanen kauyen da ke gudanar da sallar asuba.

Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim-Matane ya tabbatar wa jaridar The Nation faruwar harin.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Asali: Legit.ng

Online view pixel