Taraba: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴan tsohon SSG 6, dogarinsu da direba

Taraba: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴan tsohon SSG 6, dogarinsu da direba

  • 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da 'ya'yan tsohon sakataren gwamnatin jihar Taraba, Gebon Kataps, har su shida tare da dan sandan dake tare da su da direba
  • Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan Taraba, Usman Abdullahi ya sanar, lamarin ya faru a kauyen Jamtari da ke karamar hukumar Gashaka
  • Kataps ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace 'yan sanda suna kokarin ceto wadanda aka sace tare da cafke miyagun da suka yi aika-aikar

Taraba - 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da 'ya'yan tsohon sakataren gwamnatin jihar Taraba har su shida, Gebon Kataps, tare da dan sandan da ke basu kariya da kuma direbansu.

Guardian ta ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin amma bata tabbatar da yawan wadanda aka sace ba.

Taraba: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴan tsohon SSG 6, dogarinsu da direba
Taraba: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴan tsohon SSG 6, dogarinsu da direba. Hoto daga guardian.ng
Asali: UGC

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan, Usman Abdullahi, ya ce lamarin ya faru wurin kauyen Jamtari da ke karamar hukumar Gashaka ta jihar.

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

Yayin aukuwar lamarin, 'yan ta'addan sun sheke mutum daya, wani jami'in dan sanda da ke aiki a Jamtari ya sanar.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce rundunar ba za ta sassauta ba har sai ta ceto wadanda aka sace kuma ta cafke 'yan ta'addan.

Har ila yau,domin tabbatar da faruwar lamarin, Paul Dogoh, shugaban karamar hukumar Gashaka ya ce ya san cewa lamarin ya faru a ranar Laraba.

Kataps a yayin tattaunawa da The Guardian, ya ce an sace mutum shida daga cikin 'yan gidansu wadanda suka hada da 'ya'yan shi, diyar dan uwanshi da kuma direbansa.

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

A wani labari na daban, 'Yan bindiga sun tsinkayi yankin Mareri da ke babban birnin jihar Zamfara a ranar Juma'a kuma sun sace mata da diyar wani lakcaran kwalejin ilimi. An gano cewa, sun kwashi dukiya daga gidan malamin mai suna Dr Abdulrazak Muazu, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Ba a tabbatar da cewa Muazu ya na gida ko ba ya nan ba lokacin da masu farmakin suka shiga gidansa.

"'Yan bindigan sun bayyana a gidansa da sa'o'in farko na ranar Juma'a. Babu wanda aka kashe yayin kai farmakin amma sun kwashe kadarori na dubban naira.
"Har a yanzu ba su kira kowa ba domin sanar da kudin fansan da suke bukata. Amma lamarin ya gigita jama'ar yankin inda da yawansu suke tunanin barin gidajensu," wani mazaunin yankin mai suna Aminu Muhammad ya sanar da Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel