Sabon hari: 'Yan bindiga sun tafka barna a Zariya, sun kashe mutane sun saci dabbobi

Sabon hari: 'Yan bindiga sun tafka barna a Zariya, sun kashe mutane sun saci dabbobi

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da hallaka wasu mutane a wasu sassan Igabi da Zariya a jihar ta Kaduna
  • Hakazalika, gwamnatin ta tabbatar da sace dabbobi sama da 250 a wani yankin Rigachukum duk dai a jihar
  • Gwamna El-Rufai ya yi jimami tare da mika sakon ta'aziyya da jaje ga iyalan wadanda abin ya rutsa dasu

Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane tara tare da raunata wasu biyar da kuma sace dabbobi sama da 250 a hare-haren da suka kai a karamar hukumar Igabi da Zaria a jihar Kaduna.

An tattaro cewa 'yan bindigan sun fara kai hari ne a unguwar Kudu da Gari dake Sabon Birni a karamar hukumar Igabi inda suka kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu hudu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

Barnar 'yan bindiga a jihar Kaduna
Sabon hari: 'Yan bindiga sun tafka barna a Zariya, sun kashe mutane sun saci dabbobi | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A wani matsugunin makiyaya kuwa mai suna Ruggar Goshe da ke wajen kauyen Kangimin Sarki a Rigachikun a karamar hukumar Igabi, ‘yan bindigar sun harbe Auwal Koshe har lahira tare da sace awaki da tumaki kusan 250.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai hari wani matsugunin makiyaya a Filin Idin Barebari, karamar hukumar Zariya, inda suka kashe wani Abubakar Mohammad tare da jikkata wani Abubakar Aliyu a hakarkarinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga nan ne ‘yan bindigan suka yi awon gaba da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba a unguwar.

Kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojoji sun kashe wasu ‘yan bindiga biyu a wajen kauyen Tumbau da ke Kerawa a karamar hukumar Igabi.

Ya ce ‘yan bindigar na komawa dajin Malul ne yayin da sojojin suka tare su suka kuma ragargajesu, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

A cewarsa:

“Da yake bayyana alhininsa da rahotannin hare-haren, Gwamna Nasir El-Rufai ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalansu. Gwamnan ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa."

Rahotanni a ranar Lahadin da ta gabata sun ce kimanin mutane 7 ne suka mutu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wurare daban-daban a jihar tare da yin garkuwa da mutane sama da 40.

Jam’iyyar APC ta yi fallasa, tace wani tsohon Soja yana da alaka da ‘Yan bindiga

A wani labarin, jam’iyyar APC ta jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa akwai hannun wani tsohon Janar na gidan soja da ya yi ritaya a halin rashin tsaro.

APC mai mulki na zargin cewa wannan tsohon soja da aka ba damar hako ma’adanai a Zamfara ya taimaka wajen jawo ‘yan bindiga da ake fama da su.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Jaridar Vanguard tace Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Malam Yusuf Idris, ya bayyana wannan wajen wani taron ‘yan jarida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel