‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kwastam mai ritaya, Mohammed Zarma, a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara
  • Maharan sun sace Zarma wanda ya kasance tsohon mataimakin kwanturola janar na hukumar kwastam a gonarsa ta kiwon kifi
  • Kakakin 'yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da lamarin inda ya ce ana kokarin ceto shi

Kwara - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani shugaban kwastam mai ritaya, Mohammed Zarma, a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara a ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a Egbejila, a hanyar kauyen Obate, karamar hukumar Asa.

An yi garkuwa da mutumin wanda ya kasance mataimakin kwanturola janar na hukumar kwastam a gonarsa ta kiwon kifi.

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara
‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa da wani mazaunin yankin ya fitar, maharan sun mamaye gonar da muggan makamai.

Kara karanta wannan

Kungiya ga Ortom: Ka mayar da hankali wurin biyan albashi a Benue, maimakon matsawa Buhari

"Sun shigo gonar a kafa sannan suka tsere da mutumin ta cikin dajin da ke sada kauyukan Ogele, Pampo da Arowosaya. Don haka, muna kira ga jami'an tsaro da su gaggauta nadesu."

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin 'yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce ana kokarin ceto shi.

Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Tuesday Assayomo ya umurci jami'ansa da su tabbatar sun kubutar da jami’in Kwastam din da aka yi garkuwa da shi ba tare da wani rauni ba, rahoton Vanguard.

Ajayi ya ce:

"Rundunar ta tura abubuwan da suka dace, na mutane da kayan aiki don ceto shi. Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka yi garkuwa da shi a gonarsa da ke Egbejila da misalin karfe 5:30 na ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC yayin da fusatattun mambobin jam’iyyar suka maka Buni a Kotu

"A ziyarar da jami'an 'yan sandan suka kai wurin da lamarin ya faru, an samo harsashi guda hudu da babu komai a ciki."

Direban NAPEP ya shiga hannu yayin da ya yi garkuwa da kansa, ya nemi kudin fansa

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Gombe sun damke wani matashi mai suna Haliru Aliyu, mai shekaru 32 bayan ya yi garkuwa da kansa sannan ya nemi N500,000 a matsayin kudin fansa daga 'yar'uwarsa.

An kama Aliyu tare da wani Ahmed Ladan mai shekaru 42 bayan jami'an rundunar sun samu bayanai kan abun da mai laifin ya aikata, jaridar PM News ta rahoto.

A cewar wata sanarwa daga Mary Malum, kakakin rundunar 'yan sandan Gombe, ana nan ana binciken wadanda ake zargin biyu kan laifukan da ke nasaba da hada kai wajen ta'addanci, razanarwa, garkuwa da mutane da kuma karbar kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel