Kaduna: El-Rufai ya ba da umarni ga makarantun gwamnati a koma karatun kwana 4

Kaduna: El-Rufai ya ba da umarni ga makarantun gwamnati a koma karatun kwana 4

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta rage ranakun karatu ga makarantun gwamnati a fadin jihar sabodda dalilan tsaro
  • Wannan na zuwa neyayin da gwamnatin a baya ta bayyana manufarta wajen tabbatar da jin dadin aiki da inganta tsaro
  • Hakazalika, gwamnati ta sanar da ranar da dalibai za su ci gaba da karatu a zangon karatun na shekarar 2021/2022

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkan makarantun gwamnati da su koma aikin kwanaki hudu a mako, yayin da za a bude makarantun a ranar 10 ga watan Janairu a zango na biyu na shekarar 2021/2022.

Kwamishiniyar Ilimi, Halima Lawal, ta ba da wannan umarni ne a Kaduna ranar Lahadi a cikin sanarwar dawowa karatu a zango na biyu na shekarar 2021/2022, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babban taro: Gwamnonin APC za su gana da Shugaba Buhari don tsayar da rana

Gwamna ya umarci a rage ranakun karatu a Kaduna
Kaduna: El-Rufai ya ba da umarni ga makarantun gwamnati a koma karatun kwana 4 | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya nakalto cewa, gwamnatin jihar Kaduna a ranar 1 ga Disamba, 2021, ta sauya tsarin aiki zuwa kwanaki hudu mako.

Ta ce ya kamata dukkan iyaye da kuma sauran jama’a su lura cewa gwamnatin jihar ta amince da ranar 10 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a ci gaba da zaman karatun a zango na biyu na shekarar 2021/2022.

Jaridar The Cable ta rahoto Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai kan harkokin yada labarai, yana cewa, matakin rage ranakun zai shafi kamfanoni masu zaman kansu da ke jihar.

Ya bayyana cewa an tsara matakin ne don taimakawa wajen habaka nagartar aiki da habaka daidaiton rayuwar aiki.

A bangaren marantu, Halima Lawal, a sanarwar ta na baya-bayan nan, ta bukaci makarantun gwamnati na jihar da su bi sabon tsarin.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Gwamnatin Zamfara ta sake bude wasu kasuwanni 4

A kalamanta:

“Ma’aikatar ilimi tana sa ran dukkan shugabanni makarantun sakandare da na firamare su karbi daliban makarantun kwana a ranar Lahadi, 9 ga watan Janairu, da dalibai gama gari a ranar Litinin, 10 ga Janairu, 2022, bi da bi.”
"Ma'aikatar ta kuma shawarci iyaye, masu kula da yara, da dalibai da su bi duk ka'idojin kiwon lafiyar jama'a ta hanyar daukar duk matakan kariya daga Korona."

Lawal ta bukaci shuwagabannin makarantun su bi tsarin karatun makaranta lafiya kamar yadda ma’aikatar ilimi ta tarayya ta ba da umarni.

Ta shawarci mambobin kwamitin tsaro na makarantu da su tabbatar da sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa.

A cewarta, za a iya a ba da rahoton barazanar tsaro a makaratntu ta wadannan lambobi kamar haka: 09034000060 ko 08170189999.

Allah yasa ba korar ma'aikata ko rage albashi zaka yi ba, CAN ta maida martani ga El-Rufai

A wani labarin, kungiyar kiristoci ta ƙasa (CAN) reshen jihar Kaduna tace tana fatan rage ranakun aiki da gwamnatin Kaduna ta yi, ba wata makarkashiya bace don sallamar wasu ma'aikata ko rage musu albashi.

Kara karanta wannan

Anzo wajen: Twitter ya cika ka'idojin Buhari, bayanai sun fito kan dage doka

Tribune Online ta rahoto cewa wannan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban CAN, Joseph John Hayab, ya fitar ranar Talata.

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ta dauki matakin rage ranakun aiki ne domin kara inganta aiki da kuma karin hutu ga ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel