Matsalar tsaro: Gwamnatin Zamfara ta sake bude wasu kasuwanni 4

Matsalar tsaro: Gwamnatin Zamfara ta sake bude wasu kasuwanni 4

  • Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da umarnin sake bude wasu kasuwanni hudu da aka garkame sakamakon matsalar tsaro a jihar
  • Kasuwannin da aka yi umurnin budewa sun hada da na Dansadau, Maradun, Bungudu da Maru
  • Wannan matakin ya biyo bayan samun rahoton daidaituwar al’amuran tsaro a yankunan

Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta amince da sake bude wasu karin kasuwanni hudu da aka rufe a jihar saboda matsalar rashin tsaro.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa umurnin ya biyo bayan samun rahotanni masu gamsarwa a kan yanayin tsaro a wadannan garuruwan da abun ya shafa.

Matsalar tsaro: Gwamnatin Zamfara ta sake bude wasu kasuwanni 4
Matsalar tsaro: Gwamnatin Zamfara ta sake bude wasu kasuwanni 4 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Tun farko dai gwamnatin jihar ta bude kasuwanni bakwai na Kaura Namoda, Kasuwar Daji, Gusau, Danjibga, Tsafe, Talata Mafara da Gummi.

Kwamishinan labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya jero karin kasuwanni hudu da za a bude da suka hada da na Dansadau, Maradun, Bungudu da Maru.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa, ya nada sabon Babban Alkali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, a garin Gusau, babbar birnin jihar Zamfara.

Dosara ya ce:

“Hukuncin sake bude kasuwannin ya zo ne bayan samun rahoton daidaituwar al’amuran tsaro a yankunan."

Ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar ta kulla yarjejeniya da shugabannin kasuwannin cewa za su sanya ido tare sa hana faruwar laifuka a kasuwannin sannan za su kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Ya bayyana godiyar gwamnatin jihar kan yadda jama’a ke bayar da hadin kai da kuma addu’o’i da suke mata.

A rahoton Aminiya, Dosara ya jinjina wa jami’an tsaro a jihar kan yadda suke namijin kokari wajen tabbatar da tsaro da kuma yaki da ’yan bindiga.

Ya kuma ce ana ci gaba da samun kyakkyawan sakamako a yaki da ake yi da ’yan ta'adda a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Mista Dosara ya kuma tabbatar wa da jama’ar cewa gwamnatin za ta ci gaba da kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Zamfara: Gwamnati ta rufe wasu gidajen biredi da man fetur da ke yi wa 'yan bindiga aiki

A wani labari, mun kawo a baya cewa kwamitin tsaro na gwamnatin jihar Zamfara, a ranar Laraba, ta bada umurnin a rufe wani gidan mai da gidan biredi da ke kananan hukumomin Gusau da Tsafe a jihar, The Cable ta ruwaito.

Abubakar Dauran, shugaban kwamitin ne ya bada wannan umurnin jim kadan bayan jami'an tsaro sun kama wasu mutum hudu da ake zargi da sayarwa yan bindiga biredi da man fetur.

Dauran, wanda kuma mashawarci na musamman ne kan harkokin tsaro ga Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, ya ce an rufe gidan man da ke Tsafe ne saboda sayarwa yan bindiga abokan huldarsu man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel