Anzo wajen: Twitter ya cika ka'idojin Buhari, bayanai sun fito kan dage doka

Anzo wajen: Twitter ya cika ka'idojin Buhari, bayanai sun fito kan dage doka

  • Bincike ya bayyana cewa, kamfanin Twitter ya cika dukkan ka'idojin da gwamnatin Buhari tasa, saura fara aiki
  • Wannan na zuwa ne bayan da kamfanin ya roki a bashi damar yin hakan zuwa farkon shekarar 2022 da muke ciki
  • Yanzu dai bayanai sun bayyana yadda kamfanin ya cika wadannan ka'idoji kamar yadda gwamnatin Najeriya ta tsara

Bincike da ingantattun rahotanni sun nuna cewa shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin tarayya ta dakatar a shekarar 2021, ana sa ran zai ci gaba da aiki nan kusa, bayan cika dukkan sharuddan da aka bayar bayan daukar tsauraran matakai.

Jaridar The Nation ta ce kwamitin kwararru da aka kafa domin warware matsalar da ke tsakanin bangarorin biyu kan abubuwan Twitter ya bayar bayan haka za a saurari batun karshe daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

Batun dakatar da Twitter a Najeriya
Anzo wajen: Twitter ya cika ka'idojin Buhari, bayanai sun fito kan dage doka | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Wata majiyar gwamnati ta bayyana cewa a karshe shafin ya cika sharudda shida da gwamnati ta gindaya na dage takunkumin da aka sanya mata a Najeriya a daidai lokacin da ake rufe kasuwancinsa a shekarar 2021.

Majiyar ta kara da cewa daga yanzu za ke kula da aikin Twitter a Najeriya tare da cewa nan ba da dadewa ba zata a bude ofishi a Najeriya.

A cewar majiyar da bata bayyana sunanta ba, akwai bukatar a samar da ofishi na zahiri domin a iya tuhuma a duk lokacin da wani abu ya faru.

Yayin da yake magana kan hasarar da bangarorin biyu suka yi da kuma hasashen da ake yi, majiyar ta ce;

“Twitter kawai ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta ba shi damar bude ofishi a shekarar 2022 saboda babu wani tanadi da aka yi a cikin kasafin kudinsa na bara. Tunda muna cikin sabuwar shekara, muna sa ran ofishin zai fara aiki nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Daga karshe: 'Yan kasa sun tafka zanga-zanga, firaministan Sudan yayi murabus

“Tare da biyan haraji, muna fatan gwamnati za ta samu karin kudaden shiga daga Twitter. Wannan haramcin ya taimaka wajen gyara abubuwan da suka faru a baya.
"Misali, Twitter yana tara makudan kudade daga Najeriya ba tare da goyon bayan doka da bin dokokin kasar mu ba.
"Duk da amfani da VPN da wasu 'yan Najeriya ke yi, kudaden shiga na Twitter sun ragu sosai saboda wannan madadin ba ya samar da kudin shiga."

Ka'idojin da aka gindiyawa Twitter, kuma tuni ya cika

A kasa mun tattaro muku sharuddan da Twitter ya riga ya cika:

  1. Bude ofis a Najeriya
  2. Samar da wakilinsu a kasar
  3. Yi rijista da Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC) / samun lasisi daga Hukumar Watsa Labarai ta Kasa
  4. Biyan haraji ga Najeriya
  5. Mai hankali ga tsaron kasa da hadin kai. Kada a raina tsaron kasa
  6. Horar da ma'aikatan IT na Najeriya da jami'an leken asiri kan yadda ake ba da rahoton cin zarafi / cin zarafi da gwamnati ta lura dashi daga Twitter

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a rikicinsu da gwamnatin Buhari

Duba da wannan, Legit.ng Hausa ta ziyarci shafin rajistar kamfanoni da kasuwanci a Najeriya ta CAC, inda ta binciki sunan Twitter, amma ba a sunan da ke nuna alamar kamfanin ya yi rajistar ba.

Baya ga Twitter, saura su NetFlix

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta bayyana shirye-shiryen ta na fitar da tsarin amfani da kafafen yada bidyo irinsu NetFlix, kamar yadda ta yi ikirarin cewa za a iya amfani da su don "haifar da hargitsi" da kuma lalata tsarin dimokradiyyar Najeriya.

A wani taro na kwanaki biyu, gwamnatin Buhari da masu ruwa da tsaki a masana'antun kirkira sun tattauna yiyuwar duba ayyukan kafafen yada bidiyo kai tsaye tare da tacewa da kayyade amfani dasu.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa shahara da kuma bukatuwa ga shirye-shiryen kai tsaye a Najeriya ya karu saboda Korona don haka za a sa ka’idoji.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wasu kasuwanni biyu a jihar Sokoto, ta kone shaguna

Asali: Legit.ng

Online view pixel