Allah yasa ba korar ma'aikata ko rage albashi zaka yi ba, CAN ta maida martani ga El-Rufai

Allah yasa ba korar ma'aikata ko rage albashi zaka yi ba, CAN ta maida martani ga El-Rufai

  • Kungiyar kiristoci CAN ta shawarci ma'aikatan jihar Kaduna su daina murna da matakin rage ranakun aiki da gwamnatin jihar ta ɗauka
  • CAN tace kamata ya yi su dage da addu'a kada gwamnatin ta rage musu albashi, ko ta sake sallamar wasu daga aiki
  • A cewar kungiyar a halin yanzun al'ummar Kaduna sun fi bukatar zaman lafiya fiye da wannan matakin

Kaduna - Kungiyar kiristoci ta ƙasa (CAN) reshen jihar Kaduna tace tana fatan rage ranakun aiki da gwamnatin Kaduna ta yi, ba wata makarkashiya bace don sallamar wasu ma'aikata ko rage musu albashi.

Tribune Online ta rahoto cewa wannan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban CAN, Joseph John Hayab, ya fitar ranar Talata.

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ta ɗauki matakin rage ranakun aiki ne domin ƙara inganta aiki da kuma karin hutu ga ma'aikata.

El-Rufai na Kaduna
Allah yasa ba korar ma'aikata ko rage albashi zaka yi ba, CAN ta maida martani ga El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

A cewar Hayab, dalilin da gwamnatin ta kafa yana da kyau amma idan ka yi nazari sosai zaka yi mamakin matakin da amfaninsa ga ma'aikata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta rahoto Yace:

"Ina shawartan ma'aikata a Kaduna su daina murna da wannan matakin tun yanzu har sai sun tabbatar da babu wata ɓoyayyar manufa da zata biyo baya."
"Ya kamata ma'aikata su tabbatar da wannan matakin ba shi da alaƙa da shirin zabtare musu albashi.
"Su tabbatar da wataran gwamnati ba zata shaki iska ta sanar da zabtare musu albashi ba sabida ta rage musu kwanakin aiki."

Hayab ya yi kira ga ma'aikatan su cigaba da addu'a kan kada wannan gwamnatin ta El-Rufai ta sake sallamar wasu daga cikinsu kafin wa'adinta ya kare.

Abinda mutanen Kaduna ke bukata - CAN

Hayab ya cigaba da cewa:

"Abun da mutanen Kaduna ke bukata daga gwamnatin El-Rufai, shine ta magance musu kalubalen tsaro da suke fama da shi."
"Me wannan matakin zai amfanar da mutane? CAN ta jihar Kaduna zata cigaba da fatan alheri da mara wa gwamnatin baya wajen inganta rayuwar al'umma."

A wani labarin na daban kuma Gwamna El-Rufai ya roki yan Najeriya kada su zaɓi jam'iyyar PDP a zaben 2023 dake tafe

El-Rufa'i ya roki al'ummar jihar Kaduna su yarda da shi, zai zabar musu wanda ya dace ya gaji kujerarsa a 2023.

Ya kuma caccaki Sanata Shehu Sani da Sulaiman Hunkuyi bisa abinda ya kira durkusad da cigaban Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel