Babbar Magana: Gwamna ya fallasa sunayen mutum 19 a matsayin wadan da ake nema ruwa a jallo

Babbar Magana: Gwamna ya fallasa sunayen mutum 19 a matsayin wadan da ake nema ruwa a jallo

  • Gwamnan Ribas ya bayyana sunayen wasu mutum 19 dake da hannu a gudanar da haramtacciyar matatar ɗanyen man fetur a jiharsa
  • Gwamna Wike ya bayyana su a matsayin masu aikata babban laifi da ake nema, kuma yace jami'an tsaro za su kame su
  • Yace gwamnatinsa ba zata huta ba har sai ta magance wannan ɗanyen aiki dake zama barazana ga rayuwar al'umma

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Lahadi, ya bayyana sunayen mutum 19 da ake nema ruwa a jallo, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Gwamnan yace mutanen na da hannu dumu-dumu a satar ɗanyen man fetur da kuma gudanar da haramtacviyar matata, wanda ya zama barazana a jihar Ribas.

A wani jawabin da ya yi wa mutanen jiha kai tsaye, Wike ya kuma umarci shugaban ma'aikatan jihar Ribas, ya tuhumi, Mista Temple Amakiri, darakta a ma'aikatar makamashi, bisa zargin hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani mummunan hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 19 a jihar Kano

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas
Babbar Magana: Gwamna ya fallasa sunayen mutum 19 a matsayin wadan da ake nema ruwa a jallo Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya kuma tabbatar wa al'ummar Ribas cewa gwamnatinsa zata ɗauki mataki don kare su daga cutarwa ta hanyar lalata duk wata ma'aikatar tace ɗanyen mai ta haram a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayyana sunayen mutanen, waɗan da suke jagorantar, "Tawagar masu satar mai da ayyukan tace shi," kuma ya kira su da waɗan da ake nema ruwa a jallo.

Su waye gwamnan ya faɗi sunayen su?

The Cable ta rahoto a jawabin Wike, ya fadi sunayen kamar haka:

"Kwamandan OSPAC, Azubike Amadi; Mista Indiya na yankin Rumuolumeni, Mista Okey na yankin Rumupareli; Mista Anderson na yankin Ogbogoro; Mista Azeruowa na yankin Ogbogoro; da kuma Kingsley Egbula, shima daga Ogbogoro."

Sauran waɗan da sunayen su ya fito daga bakin gwamna Wike, waɗan da suka fito daga yankin Isiokpo, sun haɗa da;

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

“Kemkom Azubike, Mezu Wabali, Chigozi Amadi, Opurum Owhondah, Bakasi Obodo , Opus, Galaxi Mas, Chioma, Ogondah, Soldier, Mista Chefo, da kuma Nkasi”.

Wane kokarin gwamnatin Ribas ke yi wajen dakile lamarin?

Kazalika Wike ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gano waɗan da ke da hannu a wannan aika-aika ba bisa ƙa'ida ba daga yankunan Okrika, Patakwal, Kudu maso gabashin Ribas, da kusu maso yammacin jihar.

Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba zai fallasa sunayen su, matukar ba su kai kan su ga jami'an yan sanda ba.

Gwamnan ya kuma yi kira ga mazauna jihar su kai rahoton duk wanda suka san yana da hannu a satar ɗanyen mai da haramtacciyar matata ga jami'an tsaro.

A wani labarin kuma Mutane sun mutu yayin da motar yan sanda ta yi mummunan hatsari a birnin tarayya Abuja

Jami'an hukumar yan sanda uku sun rasa rayukansu nan take yayin da motar da suke ciki ta yi hatsari a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya canza magana maimakon fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a jiharsa

Rahotanni sun bayyana cewa motar ta kucce wa diraban ne yayin da tayar ta fashe suna tsaka da sharara gudu a kan titi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel