Tashin Hankali: Wani mummunan hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 19 a jihar Kano

Tashin Hankali: Wani mummunan hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 19 a jihar Kano

  • Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Kano tace wani mummunan hatsari ya lakume rayukan aƙalla mutum 19
  • Kwamandan FRSC na jihar Kano, Mato Zubairu, yace wasu motoci biyu ɗauke da mutum 45 ne suka yi taho mu gama a Bebeji
  • Ya kara da cewa yanzun haka mutum 26 na kwance a babban asibitin garin Kura ana kula da lafiyar su

Kano - Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Bagauda, ƙaramar hukumar Bebeji, jihar Kano ya lakume rayukan akalla mutum 19.

Hukumar Kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) ita ce ta tabbatar da haka, inda ta kara da cewa wasu 19 sun ji munanan raunuka, kamar yadda Aminiya Hausa ta rahoto.

Kwamandan hukumar FRSC reshen Kano, Mato Zubairu, yace hatsarin ya faru ne da misalin karfe 7:25 na safiyar yau Alhamis.

Hatsarin mota
Tashin Hankali: Wani mummunan hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 19 a jihar Kano Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar kwamandan, wasu motoci biyu maƙare da fasinjoji ne suka yi taho mugama a dai-dai makarantar Lauyoyi dake Bagauda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium times ta rahoto a jawabinsa Yace:

"Jami'an mu na ofishin FRSC dake Bagauda, sun samu kiran gaggawa cewa wasu motoci dake ɗauke da mutum 45 sun yi hatsari a dai-dai makarantar lauyoyi (NLS)."
"Nan take jami'an suka dira wurin da lamarin ya auku, kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka fara kokarin zaro mutanen."
"Wannan hatsari ya yi sanadin mutuwar mutum 19 nan take, yayin da sauran 26 kuma suka samu raunuka daban-daban."

Shin iyalan mamatan sun samu labari?

Bugu da kari, kwamandan yace jami'ai sun kai waɗan da suka ji raunuka babban Asibitin Kura, yayin da aka miƙa gawarwakin waɗan da suka rasu ga iyalansu domin yi musu sutura.

Bayan haka, ya tabbatar da cewa motocin da suka yi hatsarin guda biyu, an miƙa su ga ofishin yan sanda dake Bebeji.

A wani labarin na daban kuma Magidanci ya lakadawa budurwa dukan tsiya, ya umarci matarsa ta kashe ta a Kano

Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta gurfanar da wani mutumi, Ahmadu Muhammad, a gaban kotu bisa zargin razana wata mace a jihar Kano.

Mai gabatar da kara, Insufekta, Abdul Wada, yace wanda ake ƙara ya lakadawa matar dukan tsiya kuma ya umarci matansa su kashe ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel