Da Dumi-Dumi: Gwamna ya fasa fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a jiharsa

Da Dumi-Dumi: Gwamna ya fasa fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a jiharsa

  • Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya gaza bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a jiharsa kamar yadda ya yi alkawari
  • Tun a ranar Litinin da ta gabata, gwamnan ya sake jaddada cewa ranar 4 ga watan Janairu, 2022 zai faɗi sunayen kowa ya sani
  • Sai dai yace gwamnatinsa zata kyale hukumomin tsaro su kammala aikin su har su kame mutanen baki ɗaya

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya gaza bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin rashin tsaro kamar yadda ya yi alkawarin yi yau Talata 4 ga watan Janairu.

Jaridar Vangaurd ta bibiyi jawabin gwamnan a wurin taron masu ruwa da tsaki na jihar Imo, wanda ya gudana a gidan gwamnatin jiha.

Amma Uzodinma ya yi kira ga sanata mai wakiltar jihar Imo ta yamma Rochas Okorocha, ya kyale shi haka nan ya jagoranci jihar Imo cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 7 yan gida daya, da wasu mutum 17 a sabon harin jihar Kaduna

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma
Da Dumi-Dumi: Gwamna ya fasa fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a jiharsa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

The Nation ta rahoto A jawabinsa gwamnan yace:

"Banbancin tsohon gwamna, Okorocha, da sauran waɗan da suka jagorancu jihar Imo shi ne, yana son ya cigaba da mulkin jihar nan bayan ya bar ofis."
"Okorocha ne kaɗai gwamnan dake son mallake wannan jihar shi kaɗai. Ya kamata ya bar ni na mulki wannan jihar a matsayin gwamna."
"Ko babu komai na girme shi, akalla ya dace ya rinka girmama ni. Ba zai yuwu mu bar mutum ɗaya ya cigaba da tafiyar da harkokin jihar mu ba."

Gwamnan ya canza magana

Maimakon bayyana sunayen, gwamnan yace zai kyale hukumomin tsaro su kammala binciken su kan masu ɗaukar nauyin rashin tsaro a jihar.

Sai dai ya baiwa mutanen jihar Imo hakuri, sannan yace:

"Ya kamata mu bar hukumomin tsaro su yi aikin su, su kammala bincike kuma su bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin rashin tsaro, kuma su kame su baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnan APC zai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Jiharsa

A wani labarin na daban kuma Khadijat yar kimanin shekara 38 ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaba Buhari a zaɓen 2023

A tarihin Najeriya ba'a taba samun mace da ta zama shugaban ƙasa ba tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.

Wata matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a babban zaben 2023 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel