Da Dumi-Dumi: Mutane sun mutu yayin da motar yan sanda ta yi mummunan hatsari a Abuja

Da Dumi-Dumi: Mutane sun mutu yayin da motar yan sanda ta yi mummunan hatsari a Abuja

  • Jami'an hukumar yan sanda uku sun rasa rayukansu nan take yayin da motar da suke ciki ta yi hatsari a birnin tarayya Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa motar ta kucce wa diraban ne yayin da tayar ta fashe suna tsaka da sharara gudu a kan titi
  • Kakakin rundnar yan sanda reshen FCT Abuja ta bayyana hatsarin a matsayin babban abun takaici da bakin ciki

Abuja - Akalla jami'an yan sanda uku ne suka rasa rayukan su a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su, a kan hanyar Kubwa-Zuba, Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hatsarin ya rutsa da jami'an Special Tactical Squad (STS) na rundunar yan sandan ƙasar nan.

Wani shaidan gani da ido, Musa, ya shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya faru ne lokacin da tayar motar yan sandan, wacce ke zuba gudu a titi, ta fashe.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa uwargidar Janar Buba Marwa, Mrs Zainab, rasuwa

Hatsarin yan sanda
Da Dumi-Dumi: Mutane sun mutu yayin da motar yan sanda ta yi mummunan hatsari a Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Musa ya bayyana cewa ba zato ba tsammani sai Motar yan sandan Hilux Van ta yi tunguragutsi ta faɗa magudanar ruwa, inda jami'an yan sanda uku suka mutu nan take, sauran kuma suka samu raunuka.

Musa yace:

"Ina gab da zan wuce ta layi na gaba, lokacin da motar yan sanda dake zabga gudu a kan titi, ba zato ba tsammani ta gaza sarrafuwa ga direba, ta yi hatsari ta faɗa magudanar ruwa, nan take yan sanda uku suka mutu."

Gudun me yan sanda suke yi?

Wani shaidan gani da ido na daban, yace ya fahimci yan sanda sun rako wani ne da zai tafi Kaduna yin wani aiki na musamman.

Yace jami'an hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) da na hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) reshen Abuja, sun dira wurin, inda suka kwashe gawarwakin zuwa wani Asibiti.

Kara karanta wannan

Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, da manyan Maluma sun taru a Kano don addu'a

Kakakin rundunar yan sanda reshen birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh, ta bayyana lamarin a matsayin wani babban abun takaici da bakin ciki.

Da take tabbatar da aukuwar hatsarin, Adeh tace ba ta san ainihin mutum nawa ne suka mutu a mummunan hatsarin ba.

A wani labarin na daban kuma GOC na rundunar soji ta 7 yace gwamna Zulum na taimaka wa sojoji ba tare da sun bukaci hakan daga gare shi ba

Mukaddashin kwamandan rundunar soji ta 7 dake yaƙi da Boko Haram, ya bayyana taimakon da Zulum ya yi wa sojoji ba tare da sun nema ba.

Manjo Janar A.A. Eyitayo, yace da irin taimakon gwamna da goyon bayansa suna matukar kara wa sojoji kwarin guiwa a fagen fama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel