Duk da yawaitar kashe-kashe, Shugaban ma'aikatan tsaro ya yi iƙirarin kalubalen ya ragu

Duk da yawaitar kashe-kashe, Shugaban ma'aikatan tsaro ya yi iƙirarin kalubalen ya ragu

  • Janar Lucky Irabor, shugaban ma'aikatan tsaro na kasar nan ya ce kashe-kashen da ake yi a kasar nan ya ragu idan aka danganta da baya
  • Irabor ya jaddada cewa, akwai salo da damammakin tabbatar da zaman lafiya da za su yi amfani da su ta yadda babu dan Najeriya da zai zauna cikin tsoro
  • Shugaban sojin kasa, Laftanal janar Faruk Yahaya, ya jaddada cewa ba za a manta da sadaukarwar sojoji maza da matan da suka rasa rayukansu wurin baiwa kasar kariya ba

FCT, Abuja - Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, ya ce duk da kalubalen tsaro, a halin yanzu kashe-kashen mutane ya ragu idan aka danganta da baya, Daily Trust ta ruwaito.

Irabor, wanda ya sanar da hakan a yayin addu'a a coci domin ranar tunawa da sojoji na wannan shekarar, ya ce kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta ya kusa zama tarihi.

Duk da yawaitar kashe-kashe, Shugaban tsaro ya yi iƙirarin kalubalen ya ragu
Duk da yawaitar kashe-kashe, Shugaban tsaro ya yi iƙirarin kalubalen ya ragu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook
Ya ce, "Zan so mika jinjina ta musamman ga sojoji ballatana tsofaffin wadanda suka saka tubali wanda a yanzu muke kai wurin kawo zaman lafiya da kuma tsaro a dukkan fadin kasar nan.
"Akwai kalubale amma kalubalen basu da yawa kamar yadda muka fara. Hakan ne ke bai wa kowa kwarin guiwa yayin da muka shiga shekarar nan.
"Akwai damammaki masu yawa da za mu tabbatar da wannan zaman lafiyan da muke ciki kuma mu kai shi matakin da babu wanda zai dinga rayuwa cikin tsoro a dukkan sassan kasar nan."

A sakonsa na fatan alheri, shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya ce an shirya wannan bikin murnar ne domin duba ga sojoji mata da maza da suka riga mu gidan gaskiya, wadanda suka sadaukar da rayukansu wurin kare zaman lafiya, hadin kai da kuma cigaban Najeriya da duniya baki daya.

Ya jaddada cewa, da yawa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sun sadaukar da rayukansu ne a yayin yakin duniya na farko da na biyu, yakin basasa, kwantar da tarzoma a fadin duniya da sauran lamurran tsaron cikin gida.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya jaddada cewa, ba za a manta da sadaukarwarsu ba kuma ana cigaba da yi musu addu'ar rahama inda ya kara da cewa za a mayar da hankali wurin kula da jinyar wadanda suka samu raunika yayin tsaro.

Farmakin Zamfara: An samo gawawwaki 143 yayin da aka cigaba da neman wasu

A wani labari na daban, a kalla gawawwaki 143 aka samo kuma aka birne sakamakon kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a ranakun Laraba da Alhamis a jihar Zamfara, Daily Trust ta tattaro.

Idan za mu tuna, 'yan ta'adda masu gudun hijira kuma yaran Bello Turji, wadanda suke gudun hijira sakamakon luguden jiragen NAF a dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi, suna hanyarsu ta hijira ne suka dinga kashe mutane.

Mazauna yankin sun sanar da Daily Trust cewa an samo gawawwakin daga daji sabda 'yan ta'addan sun ritsa jama'a yayin da suke gonakinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel