Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu

Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu

  • Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya yi martani ga kalaman Buhari na cewar ya yi iya bakin kokarinsa a kasar
  • Shehu ya ce daidai ne don shugaban kasar ya fadi haka domin sai da yan Najeriya suka yi lallashi tare da matsa masa saboda ya tsaya takara a karon farko
  • Ya ce Buhari mutum ne mai magana cikin saukin kai da raha wanda mutane suka gaza fahimtar hakan

Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin watsa labarai, Garba Shehu, ya ce yan Najeriya ne suka matsawa Shugaba Muhammadu Buhari don ya tsaya takarar shugaban kasa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Shehu na martani ne ga wasu kalamai da shugaban kasar ya yi kan shirya-shiryensa kan zaben shugaban kasa na 2023.

Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu
Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Buhari, a wata hira da aka watsa a tashar NTA a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu, ya ce ya yi iya bakin kokarinsa ga Najeriya, inda yace yana duba ga lokacin da zai huta bayan barin kujerar mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Bayan sun sha kashe shi da baki: Buhari zai kammala mulki cike da tarin nasara, Femi Adesina

Shugaban kasar ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Game da shekaru na, ina ganin sa'o'i na, yanzu suna hutawa ne, kuma ina tabbatar maka nima ina fatan ganin bayan watanni 17 nan gaba da zan samu in ɗan huta.
"Tsufa ya fara kama ni, aiki na awa shida, bakwai ko takwas kullum a ofis ba abu bane mai sauki a yanzu; akwai batun taron majalisar koli, da takardu daga jihohi daban-daban kusan ko wane mako. Gaskiya aiki ne mai wahala, amma kaman yadda na faɗa, ni na nemi aikin don haka ba zan koka ba.
"Na yi gwamna, na yi minista, kuma ga shi ina wa'adi na na biyu a matsayin shugaban kasa. Don, haka na zaga a aikin, don haka mai kuma ya rage in yi wa kasar? Na yi iya kokari na."

Da yake martani, Shehu wanda ya bayyana a shirin Channels TV na Sunrise Daily a ranar Juma'a, 7 ga watan Janairu, ya ce shugaban kasar ya yi daidai da ya ce ya yi iyakan kokarinsa da kasar, Sahara Reporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

Shehu ya ce:

"Shugaban kasar ya kan kasance mutum mai sauki sosai wasu lokutan wajen yin magana da kuma raha; ina ganin wannan shine abun da mutane suka gaza fahimta game da shi. Ya kamata su fahimci yadda aka lallashe shi da kuma matsa masa don ya yi takara a karon farko.
"Ya yi aiki a matsayin gwamna, minista da kuma shugaban kasa a mulkin soja kuma wannan shine matsayi mafi girma da zai iya kaiwa. Ya yi ritaya ya koma gida sannan yan Najeriya suka zo suka ce kaine mutumin da ya dace a wannan lokaci, muna bukatarka. Sai da aka yi lallashi.
"Don haka, eh, daidai ne ga mutumin ya ce ya yi iya bakin kokarinsa kuma lokaci yayi, wasu mutanen za su daura daga inda ya tsaya."

Bayan sun sha kashe shi da baki: Buhari zai kammala mulki cike da tarin nasara, Femi Adesina

A gefe guda, Femi Adesina ya ce Shugaban kasa Muhammadu zai kammala wa'adin mulkinsa cikin 'tarin nasara', ya koma mahaifarsa, sannan kuma ya mayar da hankali ga dabbobinsa.

Kara karanta wannan

Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

Adesina ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken 'PMB da masu hasashen gobe', wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel