Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar

Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi martani a kan sabbin hare-haren da yan bindiga suka kai kauyuka 10 a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke jihar
  • Matawalle ya ce za a tura manyan jiragen yaki da aka siyo daga Amurka zuwa jihar domin yaki da maharan
  • Ya kuma ce ya gana da shugabannin tsaro a jihar inda suka tsara wasu dabaru da za a gani a kasa

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce za a tura manyan jiragen yaki da aka siyo daga Amurka zuwa jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga manyan hare-hare da aka kai fadin kauyuka 10 a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke Zamfara.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar
Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto yadda yan bindigar da ke hijira suka farmaki al-umma inda suka kashe akalla mutane 143.

Wani ganau ya ce sojin sama basu iya tayar da maharan ba wadanda suka amfani da mazauna yankin a matsayin garkuwa.

Bayan duba sabbin sojin da aka dauka a fadin kananan hukumomi 14 a jihar a ranar Asabar, Matawalle ya yaba ma gwamnatin tarayya na ayyana yan bindiga a matsayin yan ta’adda.

Ya ce hakan zai taimaka wajen kakkabe miyagu.

Matawalle ya ce kafin ayyana su, an tilastawa sojoji amfani da wasu kayayyaki irin su jirgin yaki kan yan bindigar amma a yanzu za su iya amfani da kowani makami don share yan ta’addan, rahoton Channels TV.

Ya ce:

“Mun fara tattaunawa da manyan hukumomi kan hanyar da ya dace a bi wajen shigo da jiragen yakin jihar Zamfara don a gaggabe dukkanin yankuna idan Allah ya yarda.”

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya magantu kan yiyuwar tsayawarsa takara

Kan hare-haren bayan nan, gwamnan ya ce ya gana da Shugabannin tsaro a jihar kuma suna tsare-tsare yayin da sakamakon kokarinsu zai fito kowani dan kasa ya gani.

Ya ce:

“A jiya, mun yi wata ganawa har zuwa 12:00am, tare da kwamishinan tsaro, kwamandan soji, daraktan DSS da sauransu, mun riga mun yi tsare-tsare kuma za ku ga sakamako nan ba da jimawa ba kila zuwa ranar Litinin za ku ga abun da muka yi."

Farmakin Zamfara: An samo gawawwaki 143 yayin da aka cigaba da neman wasu

A gefe guda, mun ji cewa a kalla gawawwaki 143 aka samo kuma aka birne sakamakon kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a ranakun Laraba da Alhamis a jihar Zamfara, Daily Trust ta tattaro.

Idan za mu tuna, 'yan ta'adda masu gudun hijira kuma yaran Bello Turji, wadanda suke gudun hijira sakamakon luguden jiragen NAF a dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi, suna hanyarsu ta hijira ne suka dinga kashe mutane.

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

Mazauna yankin sun sanar da Daily Trust cewa an samo gawawwakin daga daji sabda 'yan ta'addan sun ritsa jama'a yayin da suke gonakinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel