An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

  • Tattaunawar shugaban kasa Muhammadu Buhari da gidan talabijin na Channels ya bankado wasu batutuwa masu yawa
  • Daga ciki, shugaba Buhari ya magantu kan matakan da gwamnati ta dauka wajen ganin ta dakile ayyukan 'yan bindiga
  • A bangare guda, gwamnatin ta amince da ayyana 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sunan 'yan ta'adda a hukumance

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin fatattakar ‘yan ta’adda da suka addabi yankin Arewa maso Yamma a kasar, yana mai cewa gwamnati ta riga ta dauki mataki kan hakan.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da gidan Talabijin na Channels da aka watsa a yammacin jiya Laraba 5 ga watan Janairun 2022.

Shugaban Najeriya ya magantu kan batun 'yan bindiga
Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaba Buhari yayin hirar, ya koka kan dalilin da ya sa mutanen da ke da alaka da al'adu iri daya za su yi gaba da juna.

A cewar shugaba Buhari:

“Don haka, ina tsammanin yaren da kawai suke fahimta - mun tattauna hakan sosai da hukumomin tabbatar da doka; shugabannin tsaro, Sufeto Janar na 'yan sanda - shi ne a fatattake su; 'yan ta'addan.
"Mun ayyana su 'yan ta'adda, za mu yi maganinsu a haka."

A cewarsa, an samu nasarori a yakin da ake da ‘yan bindiga a yankin, yana mai cewa ya sha ganawa da shugabannin hukumomin tsaro a wani mataki na shawo kan lamarin.

Channels Tv ta ruwaito shugaban na Najeriya yana kara cewa:

"Kuma na yi imanin idan ka je wadannan yankuna na Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a cikin makonni hudu da suka gabata an samu ci gaba a harkar tsaro."

Kalaman shugaban kasar kan ‘yan bindiga a yankunan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta ayyana masu aikata laifuka a matsayin ‘yan ta’adda.

Meye matakan da gwamnati ke dauka?

Kafin wannan mataki, a karshen shekarar da ta gabata ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda biyo bayan wani kudiri da gwamnatin tarayya ta shigar a gabanta ta hannun ma’aikatar shari’a.

Wannan ci gaban ya biyo bayan kiraye-kirayen da aka yi daga bangarori da dama kan gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.

Baya ga manyan ‘yan Najeriya, majalisar ta kuma bukaci shugaba Buhari da ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

A baya ma dai Majalisar Dokokin Jihohi ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta haramta ayyukan barayin da suka yi garkuwa da daruruwan mutane tare da kashe wasu a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

A rahotonmu na baya kunji cewa, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana aikin ‘yan bindiga a matsayin aikin ta’addanci a hukumance, kamar yadda FIJ ta tattaro.

Abubakar Malami, SAN, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a ranar Talata.

Ya ce ofishinsa na aiki don duba hukuncin da kotu ta yanke wanda ya umarci gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel