Zamfara: 'Yan daba sun kai farmaki gidan talabijin, sun raunata edita tare da lalata kayan aiki

Zamfara: 'Yan daba sun kai farmaki gidan talabijin, sun raunata edita tare da lalata kayan aiki

  • 'Yan daban sun kutsa ofisoshin gidan jarida da talabijin na Thunder Blowers Online da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara
  • Maharan kamar yadda suka sanar, an tura su ne domin koyawa wani edita hankali amma sai ba su tarar da shi ba
  • A nan suka raunata Edita Mansur Rabiu, suka sace wayar wani edita tare da tarwatsa wasu daga cikin kayayyakin aikinsu

Gusau, Zamfara - 'Yan daba dauke da makamai sun kutsa ofishin Thunder Blowers Online, ofishin jaridar yanar gizo da gidan talabijin da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Premium Times ta gano cewa, maharan sun tsinkayi ofisoshin a daren Litinin, sun illata edita Mansur Rabiu tare da tarwatsa wasu kayayyakin aikinsu.

A wata takardar da Zahradeen Zarumi, daya daga cikin shugabannin gidan talabijin din da jaridar ya sa hannu kuma ya fitar, ya ce sun je neman wani ma'aikacinsu ne domin "koya masa darasi."

Zamfara: 'Yan daba sun kai farmaki gidan talabijin, sun raunata edita tare da lalata kayan aiki
Zamfara: 'Yan daba sun kai farmaki gidan talabijin, sun raunata edita tare da lalata kayan aiki. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Sun ce an turo su ne domin koyawa daya daga cikin ma'aikatanmu, Abdul Balarabe, darasi. Amma ba ya nan lokacin da suka zo. Hakan ne yasa suka fara cin zarafin ma'aikatan da ke nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wani edita Mansur Rabiu ya samu rauni kuma 'yan daban sun yi awon gaba da wayar wani ma'aikaci, Sulaiman Dan Aljanna, tare da na'urarsa mai kwakwalwa," takardar tace.

Takardar ta kara da cewa, gidan talabijin din da jaridar basu da masaniya kan wanda ya turo 'yan daban, Premium Times ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa kira da sakon kar ta kwana da aka tura masa ba kan farmakin.

Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su

A wani labari na daban, Bello Turji, gagararren dan bindigan jihar Zamfara, a ranar Litinin ya sako mutane 52 wadanda suka dade a hannunsa, wata majiya ta tabbatar wa da Daily Trust hakan.

"Wadanda aka sako din a halin yanzu ana fito da su daga daji zuwa wani wuri da aka yi yarjejeniya inda daga nan za a kai su garin Shinkafi.
"Motoci sun yi layi kuma an umarce su da su fara tafiya hanyar Maberiya, wani yanki da ke da nisan kilomita 5 daga gabashin garin Shinkafi," wani mazaunin yankin da ya bukaci a bye sunansa ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel