Direban NAPEP ya shiga hannu yayin da ya yi garkuwa da kansa, ya nemi kudin fansa

Direban NAPEP ya shiga hannu yayin da ya yi garkuwa da kansa, ya nemi kudin fansa

  • Wani direban adaidaita sahu mai suna Haliru Aliyu, mai shekaru 32 ya shiga hannun 'yan sanda a jihar Gombe
  • Hakan ya biyo bayan kitsa garkuwa da kansa da yayi sannan ya nemi yayarsa ta biya N500,000 a matsayin kudin fansa
  • Haliru dai ya siyar da keken adaidaita da surukarsa ta bashi bayan durkushewar kasuwancinsa don haka ta nemi ya biya ta, kan haka ne ya sace kansa

Gombe - Rundunar 'yan sandan jihar Gombe sun damke wani matashi mai suna Haliru Aliyu, mai shekaru 32 bayan ya yi garkuwa da kansa sannan ya nemi N500,000 a matsayin kudin fansa daga 'yar'uwarsa.

An kama Aliyu tare da wani Ahmed Ladan mai shekaru 42 bayan jami'an rundunar sun samu bayanai kan abun da mai laifin ya aikata, jaridar PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ka yi daidai: Shehu Sani ya goyi bayan Buhari kan watsi da batun 'yan sandan jiha, ya fadi dalili

Direban NAPEP ya shiga hannu yayin da ya yi garkuwa da kansa, ya nemi kudin fansa
Direban NAPEP ya shiga hannu yayin da ya yi garkuwa da kansa, ya nemi kudin fansa Hoto: The Cable
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa daga Mary Malum, kakakin rundunar 'yan sandan Gombe, ana nan ana binciken wadanda ake zargin biyu kan laifukan da ke nasaba da hada kai wajen ta'addanci, razanarwa, garkuwa da mutane da kuma karbar kudi.

Ta ce matsalar ta fara ne lokacin da direban adaidaitan ya siyar da keken da aka bashi don rufa asirin kansa, jaridar The Cable ta rahoto.

Mary ta ce:

"Surukar wanda ake zargin na farko, Haliru Aliyu na Tudun Wada quarters Gombe ta bashi wani keken adaidaita sahu bayan kasuwancinsa ya durkushe.
"Sai dai, wanda ake zargin ya zo ya siyar da keken kan N250,000 ba tare da sanin mai shi ba.
"Lokacin da mai shi ta tambaye shi ina keken ko kudinta, sai mai laifin ya ki kawo kowanne daga ciki.

Kara karanta wannan

Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da 'yar uwarsa ke binsa

"Saboda kunyar hakan, a cewarsa, a ranar 30 ga watan Disamba, 2021, sai wanda ake zargin ya je gidan abokinsa, wanda ake zargi na biyu, Ahmed Ladan, inda suka hada kai sannan suka kitsa garkuwa da Haliru Aliyu da nufin karbar kudi N500,000 a hannun 'yayarsa mai suna Zainab Aliyu mai shekaru 42, don ya samu ya biya kudin."

An damke budurwar da ta sace kanta, ta bukaci kudin fansan N30m

A gefe guda, wata budurwa, Ujunwa Offiah, ta shiga hannun jami'an hukumar yan sandan jihar Legas kan laifin hada baki da saurayinta, Blessed Ifesinachi, wajen karyan cewa an saceta don karban kudi daga wajen iyalanta.

Ujunwa ta bukaci kudin fansan N30million daga wajen iyayenta.

Hakazalika yan sandan sun damke wanda akayi amfani da wayansa wajen cinikin kudin fansa da iyayen yarinyan, Precious Chukwu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel