An damke budurwar da ta sace kanta, ta bukaci kudin fansan N30m

An damke budurwar da ta sace kanta, ta bukaci kudin fansan N30m

- Saboda yawaitan garkuwa d amutane a cikin al'umma, matasa sun fara garkuwa da kawunansu

- Wannna labarin wata budurwa da ta hada baki da saurayi wajen garkuwa ne

- Alhali bata san saurayin na son yin amfani da ita bane

Wata budurwa, Ujunwa Offiah, ta shiga hannun jami'an hukumar yan sandan jihar Legas kan laifin hada baki da saurayinta, Blessed Ifesinachi, wajen karyan cewa an saceta don karban kudi daga wajen iyalanta.

Ujunwa ta bukaci kudin fansan N30million daga wajen iyayenta.

Hakazalika yan sandan sun damke wanda akayi amfani da wayansa wajen cinikin kudin fansa da iyayen yarinyan, Precious Chukwu.

Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Hakeem Olados, yayin bayyana masu laifin a hedkwatar hukumar a ranar Litinin, ya ce har yanzu ba'a samu nasarar damke saurayin, Ifeshinachi, ba.

Odumosu yace, "Wannan laifin cuta da garkuwa da kai ne, kuma mutumin ya jagoranci wannan lamarin, wanda direban Uber ne ya gudu. Muna nemansa saboda shi ya hada kai da wadannan matan biyu."

"Sai yayi amfani da wayar wata budurwarshi kuma, Precious (Chukwu), wajen kira iyayen Offiah, yana mai sanar da su cewa an yi garkuwa da diyarsu."

"Ya bukaci N30m daga wajen iyayen Offiah don a sake ta, kuma yayin ciniki, sun yarje kan N700,000. Yayinda aka je ajiye kudin, muka shiga aiki kuma muka damke Offiah da Precious."

KU KARANTA: An sauke dukkan shugabannin jam'iyyar APC a fadin tarayya

A cewar Punch, Offiah ta ce kawai wasa take masa, ba tayi tunanin ya dauki abin da gaske ba.

An damke budurwar da ta sace kanta, ta bukaci kudin fansan N30m
An damke budurwar da ta sace kanta, ta bukaci kudin fansan N30m Credit: sahararepeorters.com
Source: UGC

KU KARANTA: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC

A wani labarin daban, Rashidat, matar Sheriff Ahmed, mai shekaru 44, ta zargi mijinta da takura mata a kan yadda take shiga.

Ahmed ya maka matarsa a kotu, inda yake bukatar su rabu sakamakon rashin kamun kanta da kuma mummunar shiga.

Ya kai korafin a wata kotu da ke Igando ranar Litinin, inda ya zargeta da lalata da wani dan sanda, The Cable ta wallafa.

A cewarsa, ya so ya fatattaki matarsa, amma yadda 'yan uwa da abokan arziki suka sanya baki yasa ya hakura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel