Katsina: ‘Yan bindiga sun afka Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da yaran ta 2

Katsina: ‘Yan bindiga sun afka Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da yaran ta 2

  • A daren Talata ne ‘yan bindiga su ka afka garin Makurdi da ke karkashin karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina
  • An samu rahotanni akan yadda su ka halaka mutane biyu sakamakon harin sannan su ka sace wata mata tare da yaranta guda biyu
  • Duk da kokarin sanar da ‘yan sanda halin da ake ciki, ba su bayyana ba har sai da ‘yan bindigan su ka kashe na kashewa su ka tsere

Jihar Katsina - ‘Yan bindiga sun afka garin Makurdi da ke karkashin karamar hukumar Malumfashi a cikin jihar da daren Talata, Vanguard ta ruwaito.

Sakamakon harin, mutane biyu sun rasa rayukansu sannan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wata mata da yaranta biyu.

Kara karanta wannan

Maimakon mika wa 'yan sanda, 'yan banga sun hallaka 'yan leken asirin 'yan bindiga a Zamfara

Katsina: ‘Yan bindiga sun afka Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da yaran ta 2
'Yan bindiga sun kai hari a Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da 'ya'yan 2. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun isa garin ne da yawansu don sun wuce goma kamar yadda majiyar da ta sanar da Vanguard ta shaida.

Ta ce:

“Sun afka gidan Alhaji Magaji Mallaha Makurdi su na harbi ko ta ina kafin daga baya su ka same shi da alburushi a tsakanin idanunsa da hanci.”

Sun halaka wani ma’aikacin lafiya bayan sun yi kacibus da shi

Majiyar ta shaida yadda bayan fita daga gidan Alhaji Magaji ‘yan bindigan suka harbi wani ma’aikacin lafiya, Zaharadini, bayan sun ci karo da shi.

A cewar majiyar, marigayi Zaharadini ya gudo daga karamar hukumar Safana ne zuwa Makurdi saboda tsoron harin ‘yan bindiga tsakanin karfe 10 zuwa 11 amma duk da haka sai da ya hadu da su su ka yi ajalinsa.

Yayin tabbatar da harin, daya daga cikin yaran mamacin, Bishir Magaji ya ce:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Buhari ya yanke hukunci na ƙarshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi

“Na yi gaggawar sanar da ‘yan sanda bayan jin harbin ‘yan bindigan amma ba su iso ba sai da su ka gama aika-aikar har su ka tafi.
“Yan bindigan sun harbe mahaifina har lahira kuma sun tsere da matar mahaifina da kanni na biyu.
“Sun halaka wani Zaharadini wanda ma’aikacin lafiya ne. Ya gudo daga Safana don neman tsira daga ‘yan bindigan da su ka addabe su a can.”

An yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sanda amma abin ya ci tura

Magaji ya shaida cewa a ranar Laraba ‘yan bindigan su ka saki kanwarsa amma matar babansa da yaronta mai shekara daya su na hannunsu.

Vanguard ta yi kokarin tuntubar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah don jin ta bakinsa amma abin ya ci tura. Bai amsa waya ba har lokacin rubuta wannan rahoton.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Dakarun ‘Yan Sanda sun kubutar da mutum kusan 100 daga jejin Zamfara

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel