Da Dumi-Dumi: Buhari ya yanke hukunci na ƙarshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi

Da Dumi-Dumi: Buhari ya yanke hukunci na ƙarshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin amincewarsa akan ‘yan sandan yanki a karo na biyu saboda ya yarda cewa jihohi ba za su iya daukar nauyinsu ba
  • ‘Yan Najeriya da dama ciki har da gwamnonin sun nuna bukatar samar da ‘yan sandan jihohi sakamakon tabarbarewar rashin tsaro a cikin kasar nan
  • Sai dai akwai yankunan da suka samar da wasu jami’an tsaron na daban kamar Amotekun, Ebube Agu da sauransu don taya jami’an tsaro yaki da ‘yan ta’adda

A karo na biyu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da samar da ‘yan sandan yankuna, The Nation ta ruwaito.

Ya yarda da cewa jihohi da dama ba za su iya daukar nauyinsu ba kuma yana tsoron a yi amfani da su ta wata hanyar da bata dace ba.

Kara karanta wannan

'Dan Sanda Abokin Kowa: Lokuta 4 da ƴan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da basu sani ba manyan abin alheri

Da Dumi-Dumi: Buhari ya yanke hukunci na ƙarshe kan batun 'yan sandan jihohi
A karo na biyu, Buhari ya ki amincewa da kafa 'yan sandan jihohi. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

‘Yan Najeriya da dama sun nuna bukatar samar da ‘yan sandan ciki har da gwamnonin jihohi don kawo karshen rashin tsaro da ya yi wa kasar nan katutu.

Samar da ‘yan sandan jiha wata hanya ce ta sauya tsarin tsaro kuma tuni wasu yankuna su ka samar da tasu mafitar kamar Amotekun da Ebube Agu.

Samar da ‘yan sandan yankin ya ci karo da kundin tsarin mulki

Sai dai kundin tsarin mulki bai ba wani gwamna damar samar da wasu jami’an tsaron ba tare da basu miyagun makamai.

Yayin tattaunawa da Channels TV a ranar Talata da dare, shugaban kasa Buhari ya nuna wa gwamnoni da shugabannin kananun hukumomi cewa samar da ‘yan sandan jihohi ba dabara bane.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Dakarun ‘Yan Sanda sun kubutar da mutum kusan 100 daga jejin Zamfara

Ya nuna tsoronsa akan yadda matsawar aka dauki wannan matakin akwai wadanda za su yi amfani da damar don yin abubuwan da basu dace ba.

Gwamnatin jiha ba za ta iya biyansu ba

Kamar yadda ya ce:

“Ku nemo alakar da ke tsakanin kananun hukumomi da gwamnonin jihohi. Shin kananun hukumomi su na samun abinda ya dace su samu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar?
“Shin su na samun damar?
“Jami’an kananun hukumomi su fada muku gaskiyar rigimar da ke tsakanin kananun hukumomi da gwamnatin jiha.”

Dama ya dade yana nuna rashin amincewarsa

Dama tun a baya shugaban kasa ya nuna rashin amincewarsa da samar da ‘yan sandan yanki.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a 2018, ya ce yana son a fara tuntubar kundin tsarin mulki a ji abinda ya ce.

Idan kundin tsarin mulkin ya amince sai a amince kuma a tabbatar.

Ya ce shin ko an san sau nawa suke tura kudade ga jihohi don samun damar biyansu albashi?

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Ya tambaya idan jihohi su na samun damar biyan ma’aikatansu a kan lokaci. Kuma a haka ake so a karo yawan ‘yan sanda.

Ya nuna rashin amincewarsa yace jihohi ba za su iya biyan ‘yan sandan albashinsu ba.

Kamar yadda yace, babu yadda za ayi a horar da mutum da bindiga da makamai sannan a ki biyansa albashi, tabbas reshe zai iya juye wa da mujiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel