Shugabanci ba na mashiririta da zaman kashe wando bane, APC ta yi wa Shehu Sani martani

Shugabanci ba na mashiririta da zaman kashe wando bane, APC ta yi wa Shehu Sani martani

  • Jam’iyyar APC ta jihar Kaduna ta yi wa Sanata Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya wankin babban bargo kan bayyana burinsa ta tsayawa takarar gwamna
  • Dama sanatan ya yi wani lafazi yayin bayyana burinsa na tsayawa takarar gwamnan Kaduna inda yace zai wanke duk dattin da El-Rufai ya kawo Kaduna
  • Kakakin APC na jihar Kaduna, Salisu Tanko Wusono, ya ce ba a ba shiriritatun mutane ayyuka masu muhimmanci musannan mara abin yi sai wallafe-wallafe a kafafen sada zumunta

Kaduna - Jam’iyyar APC, reshen jihar Kaduna ta mayar da Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya martani akan maganganunsa, TheCable ta ruwaito.

Yayin bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP, ya ce idan aka zabe shi a matsayin gwamna zai wanke duk wani dattin da gwamna El-Rufai ya kai jihar Kaduna da sunan gyara ko canji.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

Shugabanci ba na mashiririta da zaman kashe wando bane , APC ta yi wa Shehu Sani martani
Shugabanci ba na mashiririta da zaman kashe wando bane , APC ta yi wa Shehu Sani martani. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A takardar ta ranar Litinin, Salisu Tanko Wusono, kakakin APC na Kaduna ya ce “ana ba ayyuka masu muhimmanci ne ga wadanda suka san abinda su ke yi ba,” inda ya kara da cewa ba aikin “marasa aikin yi bane ma’abota wallafe-wallafe a yanar gizo”.

Kowa ya san tsohon sanatan da wallafe-wallafe akan abubuwan da suka zama na surutu a shafukansa na kafar sada zumunta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wusono ya ce, jihar Kaduna tana bukatar mutanen da suka dace ba wadanda idan aka ba su mulki zasu yi yadda suka ga dama ba.

“Aikin gwamna ba na wasa bane, aiki ne na wadanda suka san abinda su ke yi, masu hankali da sanin siyasa. Ba aikin marasa aikin yi ba sai wallafar yanar gizo bane wadanda su ke tunanin surutun jama’a ne zai sa su dace da shugabanci ba,” a cewarsa.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

“Ba kuma aikin ma’aikatan gwamnatin da babu abin arzikin da suka tsinana wa jama’a ba ne tsawon lokaci. Ba na mutanen da suka kwashe shekaru 2 a kan mulki ba tare da sanin abinda ya dace su yi bane face daukar wanka da shiga sutturu ba.
“Alamu sun nuna cewa shekarun da PDP ta yi a baya ta yi da na saninsu, amma kuma mutanen jihar Kaduna sun ci gaba.”

Kakakin APC din ya ce mulkin El-Rufai ya ciyar da jihar gaba ta inda ba a yi zato ba.

“Gwamnatin Nasir El-Rufai ta APC ce ta kammala kwangilar hanyoyin ruwan Zaria a ranar 27 ga watan Mayun 2017 wacce gwamnonin PDP biyu bayan gwamna Namadi Sambo su ka zubar bayan ya fara ta lokacin yana mataimakin shugaban kasar Najeriya,” a cewarsa.
“Tuni aka kammala duk ayyuka biyu na hanyoyin ruwan Zaria. Yanzu ana kan aiki na uku na jan ruwa ga kananun hukumomin da ke da makwabtaka da Zaria da karamar hukumar Sabon Gari wadanda su suka fara amfana.

Kara karanta wannan

TRCN ta magantu kan shirin Buhari na fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

“An yi gyara a asibitoci da dama sannan an fadada su duk don talakawa su amfana.
“El-Rufai ne ya kaddamar da asibitocin anguwanni 255, wadanda aka cika su da kayan aiki don mata su dinga haihuwa lafiya don rage mace-macen mata da yara," TheCable ta wallafa kamar yadda takardar tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel