Gwamnan Gombe ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa, ya nada sabon Babban Alkali

Gwamnan Gombe ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa, ya nada sabon Babban Alkali

  • Gwamnatin jihar Gombe ta yi sabbin nade-nade a jihar, inda aka nada sabon babban alkalin jihar a makon nan
  • Gwmanan jihar, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana nada Joseph Awak a matsayin sabon babban alkalin rikon kwarya
  • Hakazalika, gwamnan ya nada wasu hadimai hudu a bangarori daban-daban na gwamnatinsa duk a cikin makon

Gombe - Gidan talabijin na Channels ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya rantsar da mai shari’a Joseph Awak a matsayin sabon babban alkalin jihar na rikon kwarya.

Rantsar da Joseph Awak ya biyo bayan ritayar mai shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga ne a ranar 1 ga watan Janairu.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi sabbin nade-nade
Gwamnan jihar Gombe ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa | Hoto: ait.live
Asali: Facebook

A nasa jawabin, Gwamna Yahaya ya bukaci Awak ya yi adalci ga kowa da kowa ba tare da nuna bambanci, tsoro ko son zuciya ba.

Kara karanta wannan

Kwanan nan Sojoji za su ga karshen Turji – Gwamnan Sokoto ya yi albishir a 2022

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ya jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga bangaren shari’a da ‘yan majalisa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata domin amfanin al’ummar jihar ta Arewa maso Gabas baki daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar gwamna Yahaya:

“A namu bangaren, wannan gwamnatin za ta ci gaba da baiwa bangaren shari’a da ‘yan majalisa goyon baya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata domin amfanin al’ummar jihar Gombe baki daya.
“Bari na sake nanata cewa muradin wannan gwamnati ce ta samu daidaiton alakar aiki da bangaren shari’a da na majalisar dokoki; Dole ne bangarori uku na Gwamnati su hada kai don ci gaban kasarmu da dimokuradiyyar matasan kasarmu, ko shakka babu hadin kan mu shine karfinmu."

Yayin da y ake yabawa mai shari’a Awak bisa mukaminsa na Babban Alkali, Gwamna Yahaya ya kuma yabawa tsohon Babban Alkali, Mai shari’a Mu’azu Pindiga bisa hidimar da ya yi wa jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

A halin da ake ciki, Gwamna Yahaya ya kuma rantsar da wasu mashawarta na musamman guda hudu da aka nada kwanan nan, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Mai Tangale

A wani balabrin daban, Gwamnan Gombe Muhammadu Yahaya ya nada sabon Mai Tangale, Daily Trust ta ruwaito.

An bayyana nadin Danladi Sanusi Maiyamba a ranar Laraba. Ana sa ran za a kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan kan sarautar gargajiya ta Mai Tangale a garin Billiri dake Gombe.

Kwamishina, a Ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin Masarauta, Ibrahim Jalo ya isar da amincewar Gwamnan kuma ya gabatar da nadin daga baya ga sabon Mai Tangle a Poshiya dake Billiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel