Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

  • Dubun wasu matasa ya cika inda suka shiga hannu yayin da suke kokarin bayar da 'yar shekara 14 ga dodanni
  • Samarin biyu sun yi amfani da kullin asiri wajen yaudarar budurwar zuwa wani kango domin aiwatar da mugun nufinsu
  • Ana cikin haka ne sai wani da ke wucewa ya hange su, sannan jama'a suka yi ram da su

Bayelsa - Wata matashiyar budurwa mai shekaru 14 ta tsallake rijiya da baya a ranar Litinin, 3 ga watan Janairu, lokacin da wasu matasa biyu suka yi kokarin yin asirin kudi da ita a jihar Bayelsa.

Jama'a sun damke matasan biyu masu shekaru 16 a safiyar Litinin, a garin Sagbama da ke karamar hukumar Sagbama na jihar.

Bidiyon matasa 2 da aka kama yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa
Bidiyon matasa 2 da aka kama yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

An tattaro cewa matasan sun yaudari yarinyar da kullin asirinsu zuwa wani kango domin aiwatar da mugun nufinsu, amma sai suka taki rashin sa'a yayin da wani mai wucewa ya hangesu.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da matasan Akwa Ibom, mutum 3 sun rasa rayyukansu

Da ganinsu sai yayi zargin wani tuggu suke kullawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa daya daga cikin matasan ya kasance da ga sarkin garin Amanana-Owei.

Kalli bidiyon a kasa kamar yadda shafin Facebook na Thisisbayelsa ya wallafa:

Asirin kuɗi zan yi da shi: Malamin da aka kama da sabon ƙoƙon kan mutum da ya siya N60,000

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wani wanda ya kira kansa malamin addinin musulunci mai shekaru 55, Tunde Olayiwola, ya amsa cewa ya siyo sabon kokon kan dan adama a Ajabbale, Oka a jihar Ondo, Vanguard ta ruwaito.

Olayiwola, wanda yan sanda na jihar Ondo suka yi holensa ya ce ya siyo kan bil adaman ne domin a yi masa asirin kudi.

A hirar da ka yi da shi, wanda ake zargin da ya ce shi dan asalin garin Osogbo ne a jihar Osun, ya ce ya siya kokon kan ne kan kudi N60,000 domin a masa asiri, rahoton Blueprint.

Kara karanta wannan

Bidiyon katafaren gida da maza 4 suka gina da taɓo a ƙauye, har da wurin wanka mai ƙayatarwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel