Zamfara: Jam’iyyar APC ta yi fallasa, tace wani tsohon Soja yana da alaka da ‘Yan bindiga

Zamfara: Jam’iyyar APC ta yi fallasa, tace wani tsohon Soja yana da alaka da ‘Yan bindiga

  • Jam’iyyar APC ta reshen Zamfara tayi imani cewa akwai hannun wani Janar a matsalar rashin tsaro
  • Kakakin APC na jihar Zamfara ya bayyana wannan a lokacin da ya kira taron manema labarai a Gusau
  • Yusuf Idris yace akwai wani soja da aka ba damar hako ma’adanai da ya zama ya gagari gwamnati

Zamfara - Jam’iyyar APC ta jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa akwai hannun wani tsohon Janar na gidan soja da ya yi ritaya a halin rashin tsaro.

APC mai mulki na zargin cewa wannan tsohon soja da aka ba damar hako ma’adanai a Zamfara ya taimaka wajen jawo ‘yan bindiga da ake fama da su.

Jaridar Vanguard tace Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Malam Yusuf Idris, ya bayyana wannan wajen wani taron ‘yan jarida.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Dakarun ‘Yan Sanda sun kubutar da mutum kusan 100 daga jejin Zamfara

Yusuf Idris yace hujjoji sun nuna cewa ‘yan bindigan da suka fitini Zamfara da sauran jihohin Arewa maso yamma su na sha’awar ma'adanan yankin.

Da yake bayani, Malam Idris yace akwai wasu manya da ke wannan harka da sun gagari hukuma.

‘Yan bindiga
Gungun 'yan bindiga Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin sakataren yada labarai na APC

“Daga cikin wadannan mutane da suka gagari kowa akwai wani tsohon Janar da ya yi ritaya. Shi yake mallakar 70% na wurin hako ma’adanai.”
Ina kira ga ku ‘yan jarida ku yi bincike na musamman a kan wannan batun. Abin da za su gano zai yi matukar girgiza ku, ya ba ku mamaki sosai.”

Akwai hannun 'yan siyasa?

“Haka kuma lokacin da Gwamna Matawalle yake PDP, ake fama da matsalar tsaro sosai, babu abin da ya shafi PDP da Gwamnoninta da Zamfara.”

Kara karanta wannan

Ba wani Next Level: PDP ta fusata da yadda APC ke zawarcin Jonathan

“Kuma idan za ku tuna, gwamna ya kalubalanci shugabannin jihar su zo su rantse cewa ba su da hannu, kuma ba su goyon-bayan ta’adin da ake yi.”
“Ya nemi su hada-kai da shi wajen kawo karshen matsalolin da ke addabar jihar. Sai ku fadi mani idan sun zo sun yi wannan, ku bincika ku gani."

- Yusuf Idris

An rahoto Kakakin na APC yana cewa masu hako ma’adanai na cigaba da harkokinsu ba tare da ‘yan bindiga sun kawo masu cikas ba, duk da a cikin jeji su ke.

Hamza Al-Mustapha ya yi gaskiya?

Kwanakin baya aka ji Manjo Hamza Al- Mustapha yace masu kudi da mala’u suke jawo ake fama da matsalar tsaro musamman a wasu yankin Arewacin Najeriya.

Hamza Al- Mustapha wanda ya taba zama jami’in da ke kula da tsaron Janar Sani Abacha yace matsalar ta na da alaka da wasu da aka ba damar hako ma'adanan kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel