Zamfara: Ƴan bindiga sun nemi a biya su N50m kafin su sako matar malamin jami'a da ƴaƴansa mata 2

Zamfara: Ƴan bindiga sun nemi a biya su N50m kafin su sako matar malamin jami'a da ƴaƴansa mata 2

  • ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matar wani malamin kwalejin ilimin fasaha ta jihar Zamfara da ke Gusau, Dr Abdurrazak Muazu inda suka bukaci kudin fansa Naira miliyan 50
  • Mohammed Jamilu, wani dan uwansu ya sanar da manema labarai cewa da farko naira miliyan 100 su ka bukata amma daga bisani su ka rage zuwa naira miliyan 50 duk da dai har yanzu ana ciniki don neman ragi
  • Jamilu ya ce ba matar kadai su ka sace ba, sun hada da yaranta mata biyu tun a ranar Juma’ar da ta gabata kuma har cikin gidansu da ke cikin kauyen Mareri a wajen Gusau da safe

Zamfara - Yan bindiga sun sace mata da yaran wani malami a kwalejin ilimi ta fasaha a Gusau da ke jihar, Dr Abdurrazak Muazu kuma sun bukaci kudin fansar Naira miliyan 50, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Wani dan uwansu, Mohammed Jamilu ya sanar da The Punch cewa ‘yan bindigan sun kira kuma sun bukaci a biya naira miliyan 100 ne da farko amma daga bisani sun rage zuwa naira miliyan 50.

Zamfara: ‘Yan bindiga sun bukaci N50m a matsayin kudin fansar matar wani malamin jami’a da suka sace
Masu garkuwa sun ce a biya su N50m kafin su sako malamin jami'a da matarsa da suka sace. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ya shaida:

“Da farko sun bukaci naira miliyan 100 ne amma daga baya sun rage zuwa naira miliyan 50.”

Har yanzu ana ci gaba da ciniki

Mohammed ya sanar da manema labarai cewa ana ci gaba da ciniki saboda kudin ya yi tsada dayawa.

Ya ce:

“A ina zamu samu wannan kudin? Ya yi mana yawa. Har yanzu muna ciniki da su don mu samu mu ceto su daga hannun ‘yan ta’addan saboda duk mata ne."

A ranar Juma’ar da ta gabata, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mata da yara mata 2 na malamin kwalejin ilimi ta fasaha da ke Gusau, jihar Zamfara, Dr. Abdurrazak Muazu.

Kara karanta wannan

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

Sun so sace Dr Abdurrazak ne a rashin ganinsa su ka sace matarsa da yaransa

Sun sace matarsa, Binta Umar Jabaka da yaransa mata guda biyu, Maryam Abdurrazak da Hafsat har cikin gidansu da ke kauyen Mareri a wajen Gusau, babban birnin jihar wuraren karfe dayan daren Juma’a.

Wani ma’aikacin kwalejin ya sanar da The Punch cewa har gidan Abdurrazak su ka je don sace shi amma kuma ba su gan shi ba saboda ya boye a silin din gidan bayan jin tafiyarsu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ya tabbatar da aukuwar lamarin

A cewar Lawal:

“Yan bindigan sun dira cikin gidan ta katanga duk don su sace Dr Abdurrazak suka je amma kuma ba su same shi ba saboda ya boye ta silin.
“Sai da suka bincike ko ina don sun kwashe sa’a daya daga bisani suka dauke matarsa, Binta da yaransa mata biyu, Maryam da Hafsat.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Shehu ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka jami’an su na ci gaba da bincike don ceto wadanda ‘yan bindigan suka sace.

Kara karanta wannan

Wani mutum mai shekaru 42 ya mutu suna tsakar 'gwangwajewa' da budurwarsa a ɗakin otel

Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu

A baya, kun ji cewa wata mata mai shekaru 30, wacce ta tsira bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai wa matafiyan hanyar Kaduna da su ka doshi kudu ta bayyana yadda mahaifiyarta da yaranta 4 su ka kone kurmus, Daily Trust ta ruwaito.

Matar mai suna Shafa’atu, cikin matafiyan ta shaida cewa ita da yaranta, mahaifiyarta, kaninta, da yaran ‘yan uwanta su na cikin motar a wuraren titin Sabon Birni-Isa lokacin da ‘yan bindiga su ka kai musu farmaki.

Shafa’atu, wacce yanzu haka take asibiti inda ake kulawa da lafiyarta sakamakon kunar da ta yi, ta yi hira da manema labarai duk da halin da ta ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel