Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

  • Miyagun 'yan bindiga sun dira yankin Mareri da ke Gusau a jihar Zamfara inda suka kutsa gidan wani lakcara mai suna Abdulrazak Muazu
  • Sun tattara kadarori na dubban Naira tare da tasa keyar matarsa da diyarsa inda suka yi garkuwa da su a sa'o'in farko na ranar Juma'a
  • A farmakin da miyagun suka kai, basu kashe ko rai daya ba amma har a halin yanzu ba su kira ba domin fadin kudin fansa ba

Gusau, Zamfara - 'Yan bindiga sun tsinkayi yankin Mareri da ke babban birnin jihar Zamfara a ranar Juma'a kuma sun sace mata da diyar wani lakcaran kwalejin ilimi.

An gano cewa, sun kwashi dukiya daga gidan malamin mai suna Dr Abdulrazak Muazu, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara
Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ba a tabbatar da cewa Muazu ya na gida ko ba ya nan ba lokacin da masu farmakin suka shiga gidansa.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

"'Yan bindigan sun bayyana a gidansa da sa'o'in farko na ranar Juma'a. Babu wanda aka kashe yayin kai farmakin amma sun kwashe kadarori na dubban naira.
"Har a yanzu ba su kira kowa ba domin sanar da kudin fansan da suke bukata. Amma lamarin ya gigita jama'ar yankin inda da yawansu suke tunanin barin gidajensu," wani mazaunin yankin mai suna Aminu Muhammad ya sanar da Daily Trust.

Har a lokacin rubuta wannan rahoton, ba a samu kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ba.

Zamfara: Sanata Marafa ya magantu kan zarginsa da ake da alaka da 'dan bindiga

A wani labari na daban, daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ba ya da alaka da gawurtaccen dan bindigan nan, Abdulmuminu Moossa a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Sanatan ya bukaci ‘yan sanda, jami’an hukumar DSS da sauran jami’an tsaro da su gabatar da rahoton da zai nuna alakarsa da Moossa, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce ofishin kamfen din sanatan ya saki a ranar Juma’a, ya ce lokaci ya yi da ya kamata jami’an tsaro su jajirce wurin yin bincike akan matsalar tsaron kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel