Wani mutum mai shekaru 42 ya mutu suna tsakar 'gwangwajewa' da budurwarsa a ɗakin otel

Wani mutum mai shekaru 42 ya mutu suna tsakar 'gwangwajewa' da budurwarsa a ɗakin otel

  • Wani bawan Allah ya gamu da ajalinsa yayin da ya tafi wani otel da sabuwar budurwarsa da suka hadu sati biyu da suka gabata
  • Jami'an yan sanda a birnin Nairobi sun garzaya dakin otel din sun tsinci gawar mutumin kuma sun ce babu alamar rauni a jikinsa
  • Tuni dai an dauki gawarsa an kai dakin ajiye gawarwaki na asibiti domin a yi gwajin tabbatar da musababbin mutuwarsa

Nairobi, Kenya - 'Yan sanda a birnin Nairobi na bincike kan wani lamari da ya faru a kasar inda wani mutum mai shekaru 42 ya yanke jiki ya fadi yayin lalata da budurwarsa, LIB ta ruwaito.

Wani mutum mai shekaru 42 ya mutu suna tsakar 'gwangwajewa' da budurwarsa a ɗakin otel
Wani mutum ya mutu yayin da ya ke lalata da budurwarsa a dakin otel. Hoto: LIB
Asali: Facebook

An rahoto cewa Erastus Madzomba ya rasu ne a daren ranar Laraba 29 ga watan Disamba, yayin da ya ke gwangwajewa da budurwarsa mai suna Elgar Namusia a otel din Broadway Lodgings a Kawangware.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton da yan sanda suka fitar ya nuna cewa satin su biyu da fara soyayya. Rahoton ya kara da cewa:

"Jami'an yan sanda sun garzaya zuwa inda abin ya faru suka tarar da gawar wanda abin ya faru da shi yana kwance a cikin dakin da aka ambata."

A cewar yan sandan, babu wani alamar rauni a jikinsa kuma tuni an dauki gawarsa an kai dakin ajiyar gawarwaki a asibiti don yin gwajin tabbatar da sanadin mutuwarsa, rahoton LIB.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel