Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

  • Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadiyar rasa rayukar mutane bakwai a kauyen Zhigiri a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja
  • Daga cikin wadanda abun ya ritsa da su harda wani magidanci mai suna Mallam Mu'azu Babangida, matansa biyu da kuma babban dansa
  • Mamatan na a hanyarsu na zuwa Dnaweto, wani kauye da ke makwabtaka domin halartan taron suna

Neja - A kalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a kauyen Zhigiri a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai wani magidanci mai suna Mallam Mu'azu Babangida, matansa biyu da kuma babban dansa.

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja
Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kakakin gamayyar kungiyar Shiroro, Salis Mohamed Sabo, ya fada ma jaridar cewa lamarin ya afku ne lokacin da mazauna kauyen suke hanyarsu ta zuwa Dnaweto, wani kauye da ke makwabtaka domin halartan taron suna da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kafin a gina madatsar ruwa ta Zungeru, a kan je kauyukan biyu ne ta hanyar mota saboda babu ruwa. Don haka, kafin yanzu mutum baya bukatar shiga jirgin ruwa domin hanyar a bushe take kuma mota na iya bi. Wannan na daya daga cikin kalubalen da gina madatsar ruwa ta Zungeru ta haifar.”

Ya ce har yanzu ba a gano gawar daya daga cikin mutanen da hatsarin ya cika da su ba daga ruwan, jaridar Nigerian Tribune ta kuma ruwaito.

Ya yi kira ga Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Ruwa (HYPPADEC), da ta gaggauta daukar matakan kare aukuwar lamarin tare da samar da matakan kariya da suka hada da rigunan ceto da dai sauran su.

A cewarsa hakan zai taimaka wa al’ummar yankin su da kuma dakile sake faruwar mummunan lamarin a gaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

Bayan Abinda Ya Faru, Gwamnatin Ganduje Ta Dakatar da Sufurin Jiragen Ruwa a Bagwai

A wani labarin, gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Ganduje, ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ruwa a karamar hukumar Bagwai.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne a taron majalisar zartarwa da ya gudana ranar Laraba a gidan gwamnatin jiha.

BBC Hausa ta rahoto cewa wannan na zuwa ne awanni 24 bayan jirgin ruwa ya yi hatsari a yankin ranar Talata, mutane da dama suka mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel