Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun saki babban basaraken da suka sace a Arewa

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun saki babban basaraken da suka sace a Arewa

  • Sarkin masarautar Gindiri, karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato, Charles Mato Dakat, ya samu yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi
  • An yi garkuwa da basaraken a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba, lokacin da 'yan bindiga suka kai mamaya fadarsa da tsakar dare
  • Sai dai kuma babu wani cikakken bayani kan ko an biya kudin fansar da maharan suka nema kafin sakin nasa

Filato - Masu garkuwa da mutane sun saki Charles Mato Dakat, basaraken da suka sace a jihar Filato.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Dakat wanda ya kasance sarki a masarautar Gindiri, karamar hukumar Mangu da ke jihar lokacin da suka kai farmaki fadarsa a ranar Lahadi da ya gabata.

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun saki babban basaraken da suka sace a Arewa
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun saki babban basaraken da suka sace a Arewa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Daga bisani wadanda suka sace shi din sun tuntubi iyalinsa bayan an shafe 'yan kwanaki sannan suka nemi a biya naira miliyan 500 domin sakinsa.

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

Sai dai kuma, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, basaraken ya samu yanci a safiyar ranar Juma'a, 31 ga watan Disamba.

Wata majiya ta ahlin ta tabbatarwa da jaridar batun sakin basaraken a garin Jos a ranar Juma'a.

Ya ce:

"Allah ya amsa addu'o'inmu. An saki Mai martaba, Da Charles Mato Dakat. Yana cikin koshin lafiya."

Da aka tambaye shi kan nawa aka biya masu garkuwa da mutanen kafin suka saki basaraken, majiyar ta ce:

"Abun da zan iya fada maku shine cewa rai ya fi kudi. Mun gode dukka da addu'o'inku, karfin gwiwa da kuma goyon bayanku. Godiya ta tabbata ga Allah, kan abubuwan da yayi da kuma zai ci gaba da yi."

Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto cewa kakakin 'yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar mata da sakin basaraken a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun yi awon gaba da baban sarki a jihar Arewa

'Yan bindiga da suka sace babban sarki a Arewa sun ce a biya N50m kudin fansa

A baya mun kawo cewa, masu garkuwa da suka sace babban sarkin masarautan Pyem, Charles Mato Dakat, sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 matsayin kudin fansa kafin su sako shi, The Nation ta ruwaito.

Wata majiya daga masarautar, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce masu garkuwan sun yi magana da wasu yan fadar sarkin a wayar tarho.

Majiyar ta ce maganan da suka yi bai wuce na mintuna biyar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel