Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga da suka sace babban sarki a Arewa sun ce a biya N50m kudin fansa

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga da suka sace babban sarki a Arewa sun ce a biya N50m kudin fansa

  • Miyagun masu garkuwa da mutane da suka sace Charles Mato Dakat, babban sarkin masaurautar Pyem a Plateau sun nemi kudin fansa
  • Masu garkuwar sun yi amfani da wayar sarkin sun kira iyalansa sun nemi a biya su Naira miliyan 50 kafin su sako shi
  • Yan bindigan sun sace bsaraken ne a ranar 26 ga watan Disambar 2021 a fadarsa kuma kawo yanzun gwamnatin jihar bata yi komai ba kan lamarin

Jihar Plateau - Masu garkuwa da suka sace babban sarkin masarautan Pyem, Charles Mato Dakat, sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 matsayin kudin fansa kafin su sako shi, The Nation ta ruwaito.

Wata majiya daga masarautar, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce masu garkuwan sun yi magana da wasu yan fadar sarkin a wayar tarho.

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Yanzu-Yanzu: Wadanda suka sace babban sarki a Arewa sun ce a biya N50m kudin fansa
Masu garkuwa da suka sace babban sarkin arewa sun ce a biya su N50m kudin fansa. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya ce:

"Mun yi magana da su. Babban sarkin ne ya fara kiran mu ya yi magana da mu a waya.
"Daga nan sai wadanda suka sace shin suka yi magana da mu ta wayar mai martaba.
"Sun fada mana cewa suna kula da sarkin yadda ya kamata kuma ba su da niyyar cutar da shi.
"Sun ce kawai abin da suke nema shine a basu Naira miliyan 50 kafin su sako shi. Wannan shine abin da zan iya fada a yanzu."

Majiyar ta ce maganan da suka yi bai wuce na mintuna biyar ba.

Ta cigaba da cewa:

"Sun kuma sake kira a ranar Talata, inda iyalansa suka tattauna da su suka ce za su biya Naira miliyan 30, sun yi alkawarin za su yi shawara sannan su kira."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da mota dauke da fasinjojinta ta fada magudanar ruwa

A halin yanzu da muke magana da kai muna sauraron kiran su kowanne lokaci, rahoton The Nation.

Wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun sace babban sarkin ne a fadarsa a safiyar ranar 26 ga watan Disamba

Kawo yanzu gwamnatin jihar Plateau bata ce komai ba game da sace basaraken.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel