Ba ma son 'yar mu ta sha wahala: Iyayen amarya sun fasa aurawa ango 'yarsu bayan ganin gidan da za ta zauna

Ba ma son 'yar mu ta sha wahala: Iyayen amarya sun fasa aurawa ango 'yarsu bayan ganin gidan da za ta zauna

  • Dangin amaryar da ba su so yadda gidan surukinsu yake ba sun gwammace su taimaka masa da wani gidan daban
  • Ango da danginsa da suka ji an raina musu hankali sun ki amincewa da wannan bukatar, nan take dai aka datse batun bikin
  • ‘Yan Najeriya da dama a kafar Facebook sun yi martani kan wannan lamarin da ya faru ya kuma basu matukar dariya

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Maryam Shetty a Facebook ta yada wani labari a shafinta, inda ta zayyana yadda aka fasa wani aure bayan samun karamar matsala.

Kafin ta ba da labarin, budurwar ta rubuta cewa al'adar nuna fifiko ya zama ruwan dare a yankin Arewacin kasar nan kuma iyaye ne ke aiwatar da shi.

An fasa aure saboda gidan ango ya yi banbaragwai
Ba ma son 'yar mu ta sha wahala: Iyayen amarya sun fasa aurawa ango 'yarsu bayan ganin gidan da za ta zauna | Hoto: brides.com
Asali: UGC

'Yar mu ba za ta zauna a nan ba

Ta bayyana cewa kafin a soke auren, iyayen amaryar sun ji cewa gidan angon sam bai musu ba, kuma bai dace da matsayin ’yar su ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ango da danginsa sun tubure kan bukatar gidansu amarya

Don gyara lamarin zuwa yadda suke so, dangin amarya sun ba su wani sabon gida ga ma'auratan; tayin da ango ya ki amincewa dashi tare da danginsa.

Maryam ta ce mutumin dai ba talaka bane domin shi mutum ne mai tarin ilimi kuma yana da aiki mai tsoka.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, rubutun ya tattara fiye da sharhi 400 tare da dubban dangwale bayan da aka sake yada shi ta shafin Instagram na @instablog9ja.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

fashiondoctor19 ya ce:

"OMO a rayuwar nan, kawai ka nemi kudi don kada a raina ka. Orichirichi."

foodie_mai_cooks ya ce:

"Na yarda da labarinta fah. Mutanen Arewa ba sa wasa! Amma wasu na ganin cewa 'yan matan Owerri/Igbo ne suka fi kowa tsadar aure da bukatun aure. Una never see chunchin."

beighdiva50 ya ce:

"Matsa ta isa kowane bangare na Najeriya."

officialpeaceessien94 ya ce:

"Bani da ta cewa... Mutumin tsallake rijiya ta baya."

symplychi_oma ya ce:

"Kuma waccar dukiyar da kudin gwamnati ake sacewa."

A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da tsare wata Soja da ta amince da bukatar auren wani dan bautar kasa a sansanin NYSC da ke Kwara.

Bidiyon masoyan da ke yawo an ga lokacin da suke abubuwan karbar soyayyar juna, lamarin da ya haifar da cin kalamai iri-iri a dandalin sada zumunta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar soji Onyema Nwachukwu ya aika wa TheCable Lifestyle a ranar Lahadi, ya ce sojar dai ta karya wasu ka’idojin gidan sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel