Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja

Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja

  • Rundunar 'yan sanda a Abuja sun kame wasu matasa da suka yi kokarin wawure kayayyaki a kantin Next da gobara ta kama
  • A yau ne aka samu labarin yadda gobara ta yi kaca-kaca da wani kantin sayayya a babban birnin tarayya Abuja
  • Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi 26 ga watan Disamba, inda ake zargin wasu sun yi yunkurin yin sata yayin gobarar

Abuja - Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane uku da suka yi yunkurin wawure wasu kayayyaki daga babban kanti na Next Cash and Carry da gobara ta kame a safiyar Lahadi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a yanar gizo, an ga matasa suna tura keken daukar kaya da ake zargin sun yi amfani da su wajen fitar da abubuwan suka sace.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun ceto wasu ‘yan kasuwa 48 da aka sace a hanyarsu ta zuwa Kano

'Yan sandan Najeriya sun kama barayi a Abuja
Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Sai dai da take karin haske kan halin da ake ciki a cikin wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta bakin mai magana da yawunta, Josephine Adeh, ta ce ba a sace kaya a kantin ba.

Adeh, ta bayyana cewa jami’an 'yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kai dauki cikin gaggawa domin ganin an kashe gobarar da kuma hana sace-sace a kantin.

Ta kuma bayyana cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, inda ta ce kawo yanzu ba a samu asarar rai ba.

Hakazalika ta bayyana sunayen wadanda aka kama da Ali Audu mai shekaru 18, Yahaya Yunusa mai shekaru 20 da Sahabi Abubakar mai shekaru 20.

Jaridar The Cable ta ce wasu mutane sun tafka sata yayin da ake kokarin kashe gobara, amma hukumar 'yan sanda ta yi karin bayani.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa'yan bindiga

Wani yankin sanarwar ya ce:

“Wannan ya sabawa labarin da ake yadawa domin babu wani nasarar da aka samu na wawure ko kwashe kayayyaki daga kantin."

Adeh ta bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Sunday Babaji, ya kuma ziyarci wurin tare da karamar ministar babban birnin tarayya, Ramatu Tijjani Aliyu, domin tantancewa da kuma ganin yadda lamarin ya faru.

Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta

A tun farko, fitaccen katafaren kantin Next Cash and Carry da ke Kado a babban birnin tarayya na Abuja ya na ci da wuta. Har a halin yanzu dai, ba a gano abinda ya kawo mummunan gobarar ba yayin da Daily Trust ta ziyarci wurin da lamarin ke faruwa.

A inda lamarin ke faruwa, an ga masu kashe gobara suna kokarin kashewa. A kalla motoci uku na kashe wuta aka gani a farfajiyar kantin.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel