Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda

Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda

  • Yan sandan Adamawa sun bayyana cewa al'umman kauyukan Dabna da Kwabre da ke yankin Dugwaba na karamar hukumar Hong basu tsere daga gidajensu ba
  • Rundunar ta ce babu gaskiya a rahotannin da ke cewa yan Boko Haram da yan bindiga sun kai hari yankin
  • Ta bayyana rahoton a matsayin mai batarwa da kokarin dasa tsoro a zukatan al'umma

Adamawa - Rundunar yan sanda a Adamawa ta karyata wani rahoton yanar gizo da ke cewa yan ta'addan Boko Haram da yan bindiga sun kai hari mahaifar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Kakakin yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a rahoton cewa mutanen kauyukan Dabna da Kwabre a yankin Dubgwaba da ke karamar hukumar Hong sun bar gidajensu sakamakon hare-haren.

Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda
Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda Hoto: Boss Mustapha
Asali: Facebook

Mista Nguroje ya bayyana cewa hukumar yan sandar ta tura rundunar sashin da ke yaki da ta'addanci da masu garkuwa da mutane, sannan kuma ta tura jami'an bin diddigi zuwa yankin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutane sun yi ta kansu yayin da yan bindiga suka mamaye mahaifar Sakataren FG

Ya ce zuwa yanzu babu wani rahoto daga jami'an tsaro kan cewa an kai hari yankin, jaridar Premium Times ta rahoto.

Nguroje ya ce:

"Rundunar ta samu wani bayani da ba a tantance ba cewa mutane sun yi ta kansu daga wasu kauyuka sakamakon hare-haren Boko Haram.
"A matsayinmu na rundunar tsaro, bama wasa da kowani bayani da ya shafi rashin tsaro.
"Nan take rundunar ta tura jami'an da ke yaki da ta'addanci da kuma masu leken asiri zuwa yankunan da abun ya shafa kuma zuwa yanzu babu wani rahoto na kai hari ko kuma da ke nuna mutane na barin kauyukansu."

Hakazalika da aka tuntube shi, hakimin Dugwaba, Simon Yakubu, ya yi watsi da rahoton yanar gizon inda ya bayyana shi a matsayin mai batarwa.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja

Mista Yakubu ya bayyana cewa mutane na zaune lafiya kuma suna bikin Kirsimeti a kauyukan da aka ambata a rahoton yanar gizon, PM News ta rahoto.

Ya ce:

"Rahoton na zalunci ne kuma an yi shi ne don batarwa da haifar da rudani a cikin al’ummarmu.
"Ana zargin rahoton ya fito ne daga makiya zaman lafiya da ci gaba wadanda ba sa son ganin mutane suna zaune lafiya da junansu."

Ya ce rahoton da yake samu daga kauyukan da aka ambata ya nuna cewa mutane na gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.

Mutane sun yi ta kansu yayin da yan bindiga suka mamaye mahaifar Sakataren FG

A baya mun kawo cewa mazauna kauyukan Kwapre da Dabna dake karamar hukumar Hong, jihar Adamawa sun tsere daga gidajensu saboda yawaitar harin yan bindiga.

Kauyukan Kwapre, Dabna, Lar, Zah da sauran wasu kauyuka a gundumar Garaha, nan ne sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da marigayi Birgediya Janar Dzarma Zurkusu suka fito.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun yi babban kamu, sun cafke wani kasurgumin shugaban IPOB

Dailytrust ta rahoto wani shugaban yanki a Garaha, Honorabul Hyella, na cewa mutane sun gudu daga Kwapre ne domin gudan a rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel