Sojojin Najeriya sun yi babban kamu, sun cafke wani kasurgumin shugaban IPOB

Sojojin Najeriya sun yi babban kamu, sun cafke wani kasurgumin shugaban IPOB

  • Sojojin rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar kama wani dan kasurgumin dan fafutukar kafa kasar Biafra
  • Rundunar sojin Najeriya ta ce an yi kamen ne a wani yanki da ake zargin wata sananniyar mafaka ce na 'yan kungiyar
  • A cewar rundunar, an kuma kama wasu kayayyakin aikata laifuka da suka hada da bindigogi da alburusai yayin kamen

Enugu - Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB a jihar Enugu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa sojoji sun fatattaki mazauna a yankin Akpawfu da ke karamar hukumar Nkanu ta gabas a jihar Enugu.

An tattaro cewa sojojin sun shiga unguwar ne a ranar 24 ga watan Disamba, yayin da mazauna Akpawfu ke gudanar da bukukuwan jajibirin Kirsimeti.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya sun yi babban kamu, sun cafke wani kasurgumin shugaban IPOB | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Rahoton ya ce an kama sama da matasa 50 daga cikin al’ummar yankin biyo bayan mamayar da sojojin suka yi, duk da cewa an samu rahotannin bacewar wasu matasa da dama daga yankin tun bayan harin da sojoji suka kai a watan Yuni da Yuli.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar Sojin Najeriya ta yi magana kan kama shugaban kungiyar IPOB

Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar da Legit.ng ta samo ya bayyana cewa, dakarun runduna ta 82 a wani samame tare da wasu jami'an tsaro sun gudanar da babban aiki a yankin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ta ce an kama Godwin Nnamdi ne a wani samame da suka kai a wani sansanin kungiyar IPOB da kuma ESN da ke Nkanu ta gabas.

Nwachukwu ya ce an kama Nnamdi, fitaccen shugaban kungiyar IPOB da ESN a ranar Asabar, 25 ga watan Disamba.

PM News ta rahot shi yana cewa:

“A yayin aikin na share fage, sojoji sun yi wa ‘yan adawar kawanya, lamarin da ya tilasta musu tserewa a guje, hakan ya kai ga cafke shugaban su.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Ya kara da cewa sojojin sun kwato kayayyaki daban-daban da suka hada da bindiga kirar AK 47 daya, mujalla daya mai dauke da zagayen alburusai 21 na 7. 62mm na musamman, wayar hannu daya da dai sauransu.

Shugaban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Faruk Yahaya yayin da yake yaba wa sojojin bisa nasarorin da aka samu kawo yanzu, ya umarce su da su ragargaji maboyar ‘yan ta’adda da ake zargi da aikata laifuka a yankin.

'Yan sanda sun ceto wasu ‘yan kasuwa 48 da aka sace a hanyarsu ta zuwa Kano

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta ceto ‘yan kasuwa 48 da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Kano a hanyar Birnin Gwari/Kaduna ranar Laraba, Tribune Nigeria ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan, ASP Muhammad Jalige ya fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Wata soja ta gamu da fushin gidan soja yayin da ta amince za ta auri dan bautar kasa

Sanarwar ta bayyana cewa, a lokacin da ayarin motocin ‘yan kasuwar ke tunkarar kauyen Udawa, 'yan bindiga dauke da bindigogi sun tari 'yan kasuwar, lamarin da ya kai ga sace da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel