Da Dumi-Dumi: Mutane sun yi ta kansu yayin da yan bindiga suka mamaye mahaifar Sakataren FG

Da Dumi-Dumi: Mutane sun yi ta kansu yayin da yan bindiga suka mamaye mahaifar Sakataren FG

  • Yan bindiga sun matsawa mutanen kauyukan dake karkashin gundumar Garaha dake Hong, jihar Adamawa, inda SGF ya fito
  • Mazauna yankin sun gudu baki ɗaya sai yan kaɗan domin tsira da rayuwarsu yayin da yan ta'adda suka mamaye yankunan
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Mohammed Ahmed Barde, ya tura jami'an tsaro kauyukan domin dawo da doka da oda

Adamawa - Mazauna kauyukan Kwapre da Dabna dake karamar hukumar Hong, jihar Adamawa sun tsere daga gidajensu saboda yawaitar harin yan bindiga.

Kauyukan Kwapre, Dabna, Lar, Zah da sauran wasu kauyuka a gundumar Garaha, nan ne sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da marigayi Birgediya Janar Dzarma Zurkusu suka fito.

Dailytrust ta rahoto wani shugaban yanki a Garaha, Honorabul Hyella, na cewa mutane sun gudu daga Kwapre ne domin gudan a rutsa da su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun hallaka mutane sun sace mata 33

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Mutane sun yi ta kansu yayin da yan bindiga suka mamaye mahaifar Sakataren Gwamnatin tarayya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hyella yace:

"Mutum bakwai kacal ya rage a kauyen Kwapre yanzu, sauran mutane sun koma tsakanin Hong ko Pella. Mutanen sun bayyana dalilin su, saboda mutum 52 aka sace a watan Afrilu, kuma mutum 8 ne suka dawo gida tun lokacin."
"Yanzu kuma sun gano wasu da ake zargin yan bindiga ne na yada zango a yankin, shiyasa suka gudu domin tsira da rayuwarsu."
"Sace mutane ya zama ruwan dare, yan bindiga sun fara saka wa kauyuka haraji, zuwa yanzun sun saka wa kauyukan Dabna, Sushiu, Lar da sauransu a yankin Dubana harajin zaman lafiya."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya tabbatar da hare-haren da ake kaiwa yankunan, amma bai yi cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

Sabon Hari: Yan bindiga sun shiga gida-gida, sun yi awon gaba da jama'a a Zariya

Sahara Reporters ta rahoto Kakakin yan sandan yace:

"Eh, akwai yawaitar sace mutane a kewayen waɗan nan ƙauyukan. Kuma mutane na da gaskiya su ji tsoro."
"Amma kwamishinan yan sanda, Mohammed Ahmed Barde, ya bada umarnin tura jami'ai su tsare mutanen waɗan nan yankuna."

A wani labarin na daban kuma Hotunan yadda yan daba suka yi fata-fata da wurin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara

Wasu gungun yan daban siyasa sun farmaki filin da PDP ta shirya gudanar da zaɓen shugabanninta a matakin jiha a Zamfara.

Rahotannu sun bayyana cewa yan daban sun farfasa motoci, sun lalata runfunan da aka kafa, kuma sun yi kone-kone.

Asali: Legit.ng

Online view pixel