Innalillahi: Matashi ya zuba wa mahaifiyarsa fetur ya cinna mata wuta da ranta a Neja

Innalillahi: Matashi ya zuba wa mahaifiyarsa fetur ya cinna mata wuta da ranta a Neja

  • Wani matashi mai suna Steven Jiya, ya duldula wa mahaifiyarsa, Mrs Comfort Jiya, fetur sannan ya cinna mata wuta a yayin da ta ke cikin kitchen a gidan ta, a Minna.
  • An garzaya da Mrs Jiya babban asibitin Minna don yi mata magani amma daga bisani ta ce ga garinku saboda raunin da ta yi sun yi tsanani
  • Dama ba wannan bane karon farko da Steven ya yi yunkurin halaka mahaifiyarsa amma a wannan karon ne ya yi nasara a cewar wani dan uwan matar

Niger - Wani matashi, Steven Jiya, ya cinna wa mahaifiyarsa, Mrs Comfort Jiya, tsohuwar shugaban makarantar gwamnati na mata da ke Sabon Wuse da Kwallejin Kimiyya ta Maryam Babangida, Minna, wuta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa abin bakin cikin ya faru ne a Minna, babban birnin jihar Niger.

Kara karanta wannan

Za mu kama duk yaron da muka gani yana gararamba a titi a lokacin makaranta, Yahaya Bello

Innalilahi: Matashi ya zuba wa mahaifiyarsa fetur ya cinna mata wuta a Neja
Matashi ya antayawa mahaifiyarsa fetur ya cinna mata wuta a Neja. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Steven, wanda aka ce dan kwaya ne, ya dawo daga Suleja, duk dai a Niger, a ranar Litinin sannan ya antayawa mahaifiyarsa fetur a lokacin tana kitchen din gidanta da ke Darusalam a Minna.

Wani majiya daga iyalan ta ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa ta rasu misalin karfe 3 na ranar Juma'a a babban asibitin Minna inda ake mata magani.

Dama ya dade yana yunkurin kashe ta

Wata majiya ta bayyana wa wakilin majiyar Legit.ng cewa dama tun a baya Steven ya yi yunkurin ya halaka mahaifiyarsa bai yi nasara ba amma wannan karon ya watsa mata fetur.

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar Niger, DSP Wasiu Abiodun amma ba a yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Tare Motocci a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Mutane 6, Sun Sace Da Dama

Amma Daily Trust ta tattaro cewa tuni dai babban kotun Minna ta bada umurin a tsare mata Steven.

Yan sandan GRA a Minna sun gurfanar da shi a gaban kotun.

Asirin kuɗi zan yi da shi: Malamin da aka kama da sabon ƙoƙon kan mutum da ya siya N60,000

A wani labarin, wani wanda ya kira kansa malamin addinin musulunci mai shekaru 55, Tunde Olayiwola, ya amsa cewa ya siyo sabon kokon kan dan adama a Ajabbale, Oka a jihar Ondo, Vanguard ta ruwaito.

Olayiwola, wanda yan sanda na jihar Ondo suka yi holensa ya ce ya siyo kan bil adaman ne domin a yi masa asirin kudi.

A hirar da ka yi da shi, wanda ake zargin da ya ce shi dan asalin garin Osogbo ne a jihar Osun, ya ce ya siya kokon kan ne kan kudi N60,000 domin a masa asiri, rahoton Blueprint.

Kara karanta wannan

Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel