Yan Bindiga Sun Sake Tare Motocci a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Mutane 6, Sun Sace Da Dama

Yan Bindiga Sun Sake Tare Motocci a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Mutane 6, Sun Sace Da Dama

  • 'Yan bindiga sun sake tare jerin gwanon motoccin matafiya a hanyar Kaduna-Birnin Gwari inda suka halaka a kalla mutane shi
  • Wani mazaunin garin Udawa, Mohammed Umaru, ya tabbatar da harin yan mai cewa kaninsa na cikin wadanda yan bindigan suka hallaka
  • Wannan harin na zuwa ne bayan harin da wasu 'yan bindigan suka kai a hanyar ta Kaduna-Birnin Gwari suka sace fasinjoji duk da cewa yan sanda sun ceto 40 cikinsu

Kaduna - A karo na biyu cikin awa 24, yan bindiga sun sake kai wa jerin gwanon motocci da ke dauke da matafiya hari a babban hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Ana kyautata zaton an kashe mutane shida yayin da aka sace matafiya da dama kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a Unguwar Geda, kilomita kadan daga Zankoro, wani wuri da ake fargaba a babban hanyar misalin karfe 3 na ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?

Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Sake Tare Motocci a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Matafiya
'Yan Bindiga Sun Sake Tare Matfiya a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Shida. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa ya ce kaninsa na cikin wadanda aka sace.

Ya ce:

"A halin yanzu da na ke magana da kai, zan iya tabbatar da cewa mutum shida sun mutu kuma bamu san adadin wadanda aka sace ba. Kani na yana cikin wadanda aka sace. Yan bindigan ma sun kira mu yau da yamma."

Wani mazaunin garin Udawa, Mohammed Umaru, shima ya tabbatar da cewa an kashe kaninsa.

Ya ce:

"Abin ba dadi; sun kashe kani na; yanzu muka samu gawarsa muna shirin zuwa mu birne shi."

Daily Trust ta tattaro cewa yan bindigan sun datse jerin gwannon motoccin da jami'an tsaro ke yi wa rakiya a lokacin da suka kai harin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

Kawo yanzu babu wata magana a hukumance daga rundunar yan sandan Najeriya kuma kakakin yan sandan Kaduna, ASP Jalige Mohammed bai amsa wayarsa ba.

Da farko, yan sandan sun ceto mutum 40 cikin fasinjojin da aka sace a ranar Laraba.

'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

A jiya, kun ji cewa 'yan bindiga sun sace matafiya da dama a kan hanyar Kaduna - Birnin Gwari a bayan kai musu hari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan harin da aka kai misalin karfe 11 amma an gano cewa mafi yawancin wadanda abin ya faru da su yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Wani shugaban al'umma, Muhammadu Umaru, ya shaida wa Daily Trust cewa hudu daga cikin makwabtansa suna daga cikin wadanda aka sace, ya kara da cewa yan sanda sun yi wa motoccin da suka kai 20 rakiya.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel