Za mu kama duk yaron da muka gani yana gararamba a titi a lokacin makaranta, Yahaya Bello

Za mu kama duk yaron da muka gani yana gararamba a titi a lokacin makaranta, Yahaya Bello

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce gwamnatinsa za ta kara kudin da ake ware wa bangaren ilimi a kasafin kudin shekarar 2022
  • Bayan wannan matakin, Bello ya ce ba zai amince yara su rika yawo a titi ko talla ba a lokacin zuwa makaranta
  • Kazalika, a shekarar 2021, gwamnan ya ware kaso 20 cikin 100 na kasafin kudin jihar ne ga bangaren ilimi

Lokoja, Jihar Kogi - Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa dokar ilimi ta jihar Kogi na 2020 ya haramtawa yara da shekarunsu ya kai na zuwa makaranta su rika yawo a titi a lokacin zuwa makaranta a jihar.

Bello ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jadada niyar gwamnatinsa na ganin ta rage adadin yara marasa zuwa makaranta a jihar yana mai cewa za a kama duk dalibi da aka gani yana yawo, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Za mu kama duk yaron da muka gani yana gararamba a titi a lokacin makaranta, Yahaya Bello
Laifi ne kama yaro yana gararamba a titi a lokacin zuwa makaranta, Yahaya Bello. Hoto: Photo credit: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya bada wannan tabbacin ne a wurin taron kaddamar da kamfen din gano yaran da ba su zuwa makaranta don saka su a makaranta da Hukumar Ilimi ta Tarayya, (FMoE) ta kaddamar a Lokoja.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na jihar, Honarabul Wemi Jones, ya jadada cewa ya dauki ilmi a matsayin abin da yasa a gaba a karkashin sabon tsarin gwamnatinsa.

A cewarsa, gwamnati na ganin ilmi a matsayin hanya daya til da za ta iya yantar da mutanen jihar domin su tsaya da kansu.

Ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba domin ganin ta farfado da ilimi a jihar ko da nawa za ta kashe.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel