Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun ceto wasu ‘yan kasuwa 48 da aka sace a hanyarsu ta zuwa Kano

Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun ceto wasu ‘yan kasuwa 48 da aka sace a hanyarsu ta zuwa Kano

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta yi nasarar ceto was 'yan kasuwar da aka yi garkuwa dasu a jihar
  • Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan samun rahoton sace wasu 'yan kasuwa da aka ce sun kai akalla 70
  • A rahotannin da muke samu, an ce an ceto mutane sama da 40 kuma ana ci gaba da aiki domin ceto sauran

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta ceto ‘yan kasuwa 48 da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Kano a hanyar Birnin Gwari/Kaduna ranar Laraba, Tribune Nigeria ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan, ASP Muhammad Jalige ya fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu 'yan kasuwa sama da 70 a jihar Kaduna

Taswirar jihar Kaduna
Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun ceto wasu ‘yan kasuwa 48 da aka sace a hanyarsu ta zuwa Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sanarwar ta bayyana cewa, a lokacin da ayarin motocin ‘yan kasuwar ke tunkarar kauyen Udawa, 'yan bindiga dauke da bindigogi sun tari 'yan kasuwar, lamarin da ya kai ga sace da dama.

An ce ’yan sandan da ke rakiya ga ’yan kasuwar sun samu karin goyon baya inda suka yi kaca-kaca da 'yan bindigan, lamarin da ya kai ga ceto ‘yan kasuwa 48.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar:

“Jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane arba’in da takwas zuwa cikin aminci. An dauki bayanansu kuma daga baya aka wuce da su inda suka nufa.
“Hakazalika, yana da mahimmanci a lura cewa bayanan da ke akwai ga jami'ai sun nuna cewa mace daya ba a same ta ba.

A halin da ake ciki dai ana ci gaba da kokarin ganin an ceto ta lafiya yayin da kuma za a tura karin ma'aikata zuwa yankin domin kare rayuka da dukiyoyin fararen hula a yankin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa'yan bindiga

Kwamishinan ‘yan sandan ya yabawa jami’an bisa jajircewar da suka yi wajen fuskantar hatsari yayin da suke yi wa kasarsu hidima.

Hakazalika, ya nemi su ci gaba da tsayawa tsaf domin fuskantar 'yan ta'adda da masu aikata munanan ayyuka, kamar yadda Punch ta rahoto.

'Yan bindiga sun sace wasu 'yan kasuwa sama da 70 a jihar Kaduna

A tun farko, akalla ’yan kasuwa 70 ne da ke tafiya Kano aka yi garkuwa da su a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Laraba, Tribune Nigeria ta rahoto.

An tattaro, cewa ‘yan bindiga da dama ne suka kai wa ‘yan kasuwar hari da safiyar ranar Laraba, inda suka dauke su da karfin tsiya zuwa cikin dazuzzuka.

Wani dan yankin mai suna Malam Umaru ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan kasuwar na tafiya ne a cikin ayarin motoci sama da 20 tare da rakiyar ‘yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel