Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa 'yan bindiga

Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa 'yan bindiga

  • Kimanin mutane 5,000 na wani yanki a jihar Neja a halin yanzu suna fakewa a wani tsauni saboda barnar 'yan bindiga
  • Mutanen da suka hada da yara kanana da kuma tsofaffi suna gujewa kasan gilla ne daga ‘yan bindigar da suka addabi yankin
  • Yayin da suke cikin tsaunuka, wasu mata biyu masu juna biyu daga cikin mutanen sun haihu a cikin mawuyacin hali

Kwimo, Jihar Neja - Wasu mata biyu masu juna biyu a jihar Neja sun haihu a kan wani tsauni a lokacin da suke kokarin tserewa hare-haren ‘yan bindiga a yankinsu.

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa harin da aka kai a kauyen Kwimo da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja ya sa daukacin al’ummar yankin tserewa don tsira da rayukansu.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali Bayan Ƴan Bindiga Sun Fatattaki Manoma Daga Gonakinsu, Sun Kuma Sace 2 a Abuja

Taswirar jihar Neja
Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa'yan bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar wani ganau mai suna Usman Kwimo, ba zai iya tabbatar da halin lafiyar mata masu juna biyun da jariransu ba saboda ba su da kayan aikin jinya da ake bukata don kula da su.

Kwimo ya ce kimanin mutane 5,000 na al’ummar yankin da suka hada da yara kanana ne ke fakewa a tsaunuka daban-daban a yankinsu da nufin gudun kada ‘yan ta'adda su kashe su.

Ya ce ‘yan bindigar da suka kai farmaki kauyen Kwimo akan babura kusan 120 dauke da manyan makamai, suna harbi da bindiga, sun yi awon gaba da kayan shaguna da kayayyakin gida baya ga lalata wasu kadarorin.

Da yake mayar da martani ga rahoton, sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya baiwa al’ummar jihar tabbacin cewa gwamnati a shirye take ta yi duk mai yiwuwa domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Ya ce an shirya jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a wasu al’ummomin da ke fama da rikici a jihar, kamar yadda gidan radiyon Najeriya da ke Kaduna ya tattaro.

'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

A wani rahoton, hukumomin sojan Najeriya da ‘yan sandan Najeriya sun kai wa gwamnatin jihar Kaduna rahoton cewa an kashe mutane sama da 20 a harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Giwa a jihar.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Kauran Fawa, Marke da Riheya da ke Idasu a karamar hukumar Giwa, inda suka kashe mutane sama da 20.

Ya ce an kuma kona gidaje, manyan motoci, da kananan motoci, tare da amfanin gona a gonaki daban-daban, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Asali: Legit.ng

Online view pixel