Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu 'yan kasuwa sama da 70 a jihar Kaduna

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu 'yan kasuwa sama da 70 a jihar Kaduna

  • Wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da 'yan kasuwa yayin da suke hanyar zuwa Kano daga jihar Kaduna
  • Majiyoyi sun shaida cewa, matafiyan sun kai akalla 70 a cikin motoci, kuma an zarce dasu daji a jiya Laraba
  • Har yanzu dai gwamnatin Kaduna bata yi martani kan wannan aikin ba, hakazalika 'yan sanda basu ce komai ba

Kaduna - Akalla ’yan kasuwa 70 ne da ke tafiya Kano aka yi garkuwa da su a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Laraba, Tribune Nigeria ta rahoto.

An tattaro, cewa ‘yan bindiga da dama ne suka kai wa ‘yan kasuwar hari da safiyar ranar Laraba, inda suka dauke su da karfin tsiya zuwa cikin dazuzzuka.

Taswirar jihar Kaduna
Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu 'yan kasuwa sama da 70 a jihar Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani dan yankin mai suna Malam Umaru ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan kasuwar na tafiya ne a cikin ayarin motoci sama da 20 tare da rakiyar ‘yan sanda.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai hari ne a wani wuri da ke kusa da Udawa bayan Buruku, sun yi awon gaba da ‘yan kasuwa akalla 70 daga yankin da wasu da dama daga kauyukan da ke makwabtaka da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce a ciki ya kira wayar wasu ‘yan kasuwar da suka bace amma ‘yan bindigan ne suka dauka, lamarin da ya tabbatar da cewa ‘yan kasuwar na hannunsu, kamar yadda Punch ta rahoto.

Ana ci gaba da dakon martanin ‘yan sanda a Kaduna kan lamarin har zuwa lokacin hada rahoton.

Haka kuma, har yanzu gwamnatin jihar ba ta mayar da martani kan sace ‘yan kasuwar ba.

'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

A wani labarin, Hukumomin sojan Najeriya da ‘yan sandan Najeriya sun kai wa gwamnatin jihar Kaduna rahoton cewa an kashe mutane sama da 20 a harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Giwa a jihar.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Kauran Fawa, Marke da Riheya da ke Idasu a karamar hukumar Giwa, inda suka kashe mutane sama da 20.

Ya ce an kuma kona gidaje, manyan motoci, da kananan motoci, tare da amfanin gona a gonaki daban-daban, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel