Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021

Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021

A shekarar 2021, masana’antar Kannywood ta shiga cikin jimami sosai sakamakon rashin wasu fitattun jarumanta akalla guda hudu.

Yayinda muke bankwana da 2021, mun tattaro muku jerin wadannan jarumai da suka rigamu gidan gaskiya da kuma fatan Allah ya jikansu da rahama.

Ga jerinsu:

1. Sani Garba SK

A ranar Laraba, 15 ga Disamba, 2021, Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood Sani Garba wanda aka fi sani da Sani SK rasuwa

BBC Hausa ta ruwaito cewa jarumin ya rasu ne a birnin Kano, bayan doguwar jinyar da yayi.

Rahoton yace fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar da rasuwar ɗan wasan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun fito da Malaman musuluncin da suka sace bayan an biya fiye da Naira miliyan 2

Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021
Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021
Asali: UGC

2. Ahmad Tage

Allah Ya yi wa fitaccen jarumi kuma mai daukar hoto a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Alhaji Aliyu Ahmad Tage rasuwa.

Ahmad Tage ya rasu ne a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba a jihar Kano bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021
Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021
Asali: Facebook

3. Zainab Booth

Tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hajiya Zainab Musa Booth ta rasu ne a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli a jihar Kano.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar shahararrun ’yan wasan Hausa uku wato Maryam Booth, Ramadan Booth da kuma Amude Booth.

An yi jana’izarta a safiyar Juma’a, 2 ga watan Yuli, da misalin karfe 8:00 a gidanta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road.

Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021
Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021
Asali: Instagram

4. Isiyaku Forest

Isiyaku Forest fitaccen mawaki ne a masana’antar Kannywood.

Marigayin ya fi fice a wakokin Jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Wanda ya yi wa Buhari Minista a 1984 ya kawo shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro

Ya rasu ne a ranar 4 ga Satumba bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Jaruman Kannywood 12 da Taurarinsu suka fi haskawa a 2021

A cikin shekarar nan ta 2021, akwai jaruman da tauraruwarsu ta fi haskawa sakamakon wata rawa da suka taka a wasu sabbin fina-finai ko kuma makamancin hakan.

Legit.ng ta tattaro wa masu karatu jerin jaruman Kannywood 12 da tauraruwarsu ta fi haskawa a wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel